Buhari ya dauki nauyin jan ragamar kawo karshen ta'addanci a Najeriya - Sufeton 'Yan sanda

Buhari ya dauki nauyin jan ragamar kawo karshen ta'addanci a Najeriya - Sufeton 'Yan sanda

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya damuwa tare da daura damarar tunkarar kalubale na rashin tsaro musamman kawo karshen ta'addanci da ya yi kaka-gida a jihar Zamfara kamar yadda Sufeto janar na 'yan sanda Muhammadu Adamu ya bayyana.

Buhari ya dauki nauyin jan ragamar kawo karshen ta'addanci a Najeriya - Sufeton 'Yan sanda

Buhari ya dauki nauyin jan ragamar kawo karshen ta'addanci a Najeriya - Sufeton 'Yan sanda
Source: Facebook

Babban Sufeton na 'yan sanda ya bayyana hakan ne yayin sharhi a kan yadda matsaloli na ta'addanci da shugaban kasa Buhari ya dukufa wajen kawo karshen su a wasu sassa da ya shafa cikin kasar nan.

Sufeto Adamu wanda ya ziyarci jihar Zamfara a ranar Talata ya bayyana cewa, ziyarar sa ta wajaba da manufa ta samun sahihan rahotanni daga tushe na asali domin gano ainihin bakin zaren da zai yi tasiri wajen shimfidar matakai da daurin damara.

Babban jami'in na 'yan sanda ya bayyana cewa, hukuncin da gwamnatin tarayya ta zartar na haramta hake-haken albarkatun kasa a jihar Zamfara na da nasaba ta kusa ko nesa wajen kawo kawo karshen ta'addanci a yankunan ta.

KARANTA KUMA: Gwamna El-Rufa'i ya cire dokar takaita zirga-zirga a jihar Kaduna

A yayin da babban jami'in na 'yan sanda ya bayyana shirin kawo duk karshen duk wani nau'i na ta'addanci a jihar Zamfara, Gwamna Abdulaziz Yari cikin bayyana damuwa ya ce tun daga mafarar ta mummunar ta'ada a jihar ta salwantar da rayukan kimanin Mutane 3,262 yayin da Mutane 8,900 suka rasa muhallan su.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel