Gwamna El-Rufa'i ya cire dokar takaita zirga-zirga a jihar Kaduna

Gwamna El-Rufa'i ya cire dokar takaita zirga-zirga a jihar Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufa'i, ya bayar da umurnin gaggawa na cire dokar takaita zirga-zirga daga Yamma zuwa Safiya da ya shimfida a yankunan Maraban Rido da kuma Kujama da ke karkashin karamar hukumar Chikun.

Gwamna El-Rufa'i ya cire dokar takaita zirga-zirga a jihar Kaduna
Gwamna El-Rufa'i ya cire dokar takaita zirga-zirga a jihar Kaduna
Source: UGC

Rahotanni kamar yadda jaridar Legit.ng ta ruwaito, gwamnatin jihar Kaduna ta shimfida dokar takunkumi na zirga-zirga tun a ranar 13 ga watan Maris a yankunan biyu biyo bayan barkewar wani mummunan rikici.

Cikin sanarwa Gwamna El-Rufa'i da sanadin kakakin fadar gwamnatin sa, Samuel Aruwan, a ranar Litinin ya ce a halin yanzu al'ummar yankunan Maraban Rido da kuma Kujama sun samu 'yancin ci gaba da gudanar da harkokin su na yau da kullum kamar yadda su ka saba.

Sai dai gwamnatin jihar ta ce har ila yau dokar takaita zirga-zirga daga karfe 6.00 na Yammaci zuwa 6.00 na safiya da ta shimfida a ilahirin karamar hukumar Kajuru na nan daram har zuwa lokaci na gaba, inda jami'an tsaro za su ci gaba kai komo da gudanar da sintiri na tabbatar da yiwa doka da'a.

KARANTA KUMA: Rashin cika alkawarin gwamnati: ASUP ta yi barazanar koma wa yajin aiki

Gwamnatin jihar Kaduna ta kuma mika kokon barar ta na neman dukkanin al'ummar jihar da su zauna lafiya cikin lumana da kwanciyar hankali. Ta ce ba bu kowace al'umma da za ta taka mataki na ci gaba matukar ba bu sukuni na zaman lafiya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel