Rashin cika alkawarin gwamnati: ASUP ta yi barazanar koma wa yajin aiki

Rashin cika alkawarin gwamnati: ASUP ta yi barazanar koma wa yajin aiki

Kungiyar Malaman Kwalejan fasaha na Najeriya watau ASUP, ta yi barazanar sake shiga sabon yajin aiki a sakamakon gazawar gwamnatin tarayya na aiwatar da yarjejeniyar da ta kulla tsakanin su a kwana-kwanan nan.

Rashin cika alkawarin gwamnati: ASUP ta yi barazanar koma wa yajin aiki

Rashin cika alkawarin gwamnati: ASUP ta yi barazanar koma wa yajin aiki
Source: Twitter

Babban sakataren sadarwa na kungiyar ASUP, Chris Nkoro, shi ne ya bayar da shaidar hakan bayan da kungiyar ta yanke wannan hukunci a zaman shugabannin ta da ta gudanar karo na 94 cikin kwalejin kimiyya da fasahar lafiya ta Shehu Idris da ke Makarfi a jihar Kaduna.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, kungiyar a watan Fabrairun da ya gabata ta janye yajin aikin ta na sai baba ta gani na tsawon fiye da watanni biyu da ta tsunduma sakamakon rashin aiwatar da yarjejeniyar da gwamnatin tarayya ta kulla a tsakanin su.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, Nkoro yayin ganawar sa da manema labarai bai bayar da shaidar lokacin da kungiyar su za ta tsunduma cikin sabon yajin aikin da ta nufata ba muddin gwamnatin tarayya ta ci gaba da nuna hali na rashin dattako.

KARANTA KUMA: Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin mukaman Buhari na Arewa maso Gabas

Rashin aiwatar da yarjejeniyar gwamnatin tarayya ya haifar da tasgaro na biyan basussukan albashin ma'aikata musamman a Kwalejan ilimi na jihar Abia, Kogi, Imo, Oyo, Benuwai, Nasarawa, Neja, Ekiti, Ondo da kuma Zamfara.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel