Babbar magana: Fashola ya dakatar da gina gidajen gwamnati a Abuja

Babbar magana: Fashola ya dakatar da gina gidajen gwamnati a Abuja

- Mr Babatunde Fashola, ya bayar da umurnin dakatar da ayyukan gina gidaje a Gwagwalada, babban birnin tarayya Abuja

- Rahotannin sun bayyana cewa hukumar FCDA ta rubuta "Ku dakatar da wannan ginin" a kan kusan dukkanin gine gine da ake yi a yankin

- Ya ce dakatar da ginin gidajen ya zama wajibi domin warware duk wasu matsalali da suka shafi muhalli tsakanin ma'aikatar da hukumar FCDA

Ministan wuta, ayyuka da gidaje, Mr Babatunde Fashola, ya bayar da umurnin dakatar da ayyukan gina gidaje na shirin samar da gidaje na gwamnatin tarayya, a Gwagwalada, babban birnin tarayya Abuja.

Fashola ya bayar da wannan umurnin ne a yayin zaiyarar ganewa idanuwansa yadda aikin gina gidajen ke gudana a Gwagwalada a ranar Litinin.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa hukumar bunkasa babban birnin tarayya Abuja (FCDA) ta rubuta "Ku dakatar da wannan ginin" a kan kusan dukkanin gine gine da ake yi a yankin.

KARANTA WANNAN: Tun daga yanzu: INEC za ta fitar da tsarin zaben gwamnonin Bayelsa da Kogi

Babbar magana: Fashola ya dakatar da gina gidajen gwamnati a Abuja

Babbar magana: Fashola ya dakatar da gina gidajen gwamnati a Abuja
Source: UGC

Ya ce dakatar da ginin gidajen ya zama wajibi domin warware duk wasu matsalali da suka shafi muhalli tsakanin ma'aikatar da hukumar FCDA, ta bin hanyoyin da suka dace.

"Ta hakan ne zamu girmama dokokinmu da kuma daukarsu da muhimmanci saboda wannan dai aikin ci gaba ne da gwamnati ta samar kuma ya kamata a ce mun bi doka sau da kafa," a cewar Fashola.

Ministan ya ce gina gidajen ana yinsa a jihohi 33 da ke a fadin kasar a wuraren da aka samr da filayen da zasu bada damar yin hakan.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel