Rundunar sojin sama tayi kasa-kasa da mafakar ISWAP a Tumbun Zarami, da yawa sun mutu

Rundunar sojin sama tayi kasa-kasa da mafakar ISWAP a Tumbun Zarami, da yawa sun mutu

Rundunar sojin sama (ATF) ta Ofireshon Lafiya Dole ta lalata wata mafakar 'yan ta'addar kungiyar 'Islamic State of West Africa Province (ISWAP) tare da kashe mayakan kungiyar da dama a garin Tumbun Zarami da ke gabashin jihar Borno.

ATF ta samu wannan gagarumar nasara ne a ranar Litinin, 8 ga watan Afrilu, a cigaba da atisayen 'ofireshon YANCIN TAFKI', da aka kirkira domin kakkabe burbushin kungiyar ISWAP daga kasashen gefen tekun Chadi.

Rundunar sojin sama, yayin gudanar da wani atisaye a sararin samaniya, ta gano wata mafaka da mayakan ISWAP masu yawa ke fake wa ta hanyar amfani da na'urori na musamman a jirginsu na yaki.

Rundunar sojin sama tayi kasa-kasa da mafakar ISWAP a Tumbun Zarami, da yawa sun mutu

Rundunar sojin sama tayi kasa-kasa da mafakar ISWAP a Tumbun Zarami
Source: Twitter

Bayan gano sansanin ne sai rundunar ta aika wasu jiragenta biyu na musamman (Alpha Jets) da suka yi kasa-kasa da sansanin ta hanyar yi masu ruwan bama-bamai da luguden wuta. Lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mayakan kungiyar da dama, kamar yadda Ibikunle Daramola, darektan yada labarai da hulda da jama'a na rundunar soji sama ya sanar.

DUBA WANNAN: Abinda ke ci mana tuwo a kwarya a jihar Filato - Rundunar 'yan sanda

Daramola ya bayyana cewar NAF, da dakarun sojin kasa zasu cigaba da aiki tare domin tabbatar da kawar da dukkan mambobi da lalata mafakar ISWAP.

Kalli faifan bidiyon a nan:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel