Tun daga yanzu: INEC za ta fitar da tsarin zaben gwamnonin Bayelsa da Kogi

Tun daga yanzu: INEC za ta fitar da tsarin zaben gwamnonin Bayelsa da Kogi

- INEC, ta ce a cikin makon nan za ta fitar da jadawalin tsare tsaren zaben gwamna a jihar Bayelsa da Kogi yayin da wa'adin mulkinsu zai kare a karshen wannan shekarar

- Dangane da kasafin kudin hukumar na 2019, ya ce hukumar na karbar kudadenta cif cif daga shekarar 2017 har zuwa 2018

- Sanata Suleiman Nazif, ya yabawa INEC bisa namijin kokarin da ta yi na gudanar da zaben 2019 duk da cewa ya bayyana wasu kura kurai da ya kamata a magance su

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta ce a cikin makon nan za ta fitar da jadawalin tsare tsaren zaben gwamna a jihar Bayelsa da Kogi yayin da wa'adin mulkinsu zai kare a karshen wannan shekarar.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana hakan a lokacin da ya jagoranci sauran mambobin hukumar zuwa wajen kare kasafin hukumar na 2019 gaban majalisar tarayya kan harokin hukumar zaben.

Yakubu, a yayin da ya ke kasafta kasafin kudin hukumar na 2019 da ya kai N45.4bn, ya bayyana cewa a wannan shekarar ne hukumar za ta gudanar da zaben gwamnoni a jihar Kogi da Bayelsa, sakamakon wa'adin gwamnonin da zai kare a karshen wannan shekarar.

KARANTA WANNAN: Yanzu yanzu: Yan fashi sun kai sumame wani banki a Ondo

Zaben wannan makon: INEC ta fitar da tsarin zaben gwamnonin Bayelsa da Kogi

Zaben wannan makon: INEC ta fitar da tsarin zaben gwamnonin Bayelsa da Kogi
Source: Getty Images

Dangane da kasafin kudin hukumar na 2019, ya ce hukumar na karbar kudadenta cif cif daga shekarar 2017 har zuwa 2018.

Ya ce: "A 2019, an gabatar mana da kasafin N45.5bn. Wannan kuwa dai-dai ya ke da kasafinmu na 2018 kawai dai kasafin ya zarce wanda ake ba hukumar a shekarun baya.

"A 2017, hukumar ta samu N45bn, a 2016 kuwa nan ma ta samu N45bn, a 2018 ne aka kara yawan kudin zuwa N45.5bn, kuma dai kasafin ne aka gabatar a 2018 da 2019."

A nashi bangaren shugaban kwamitin majalisar dattijai kan hukumar zaben, Sanata Suleiman Nazif, ya yabawa INEC bisa namijin kokarin da ta yi na gudanar da zaben 2019 duk da cewa ya bayyana wasu kura kurai da ya kamata a magance su.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel