Abinda ke ci mana tuwo a kwarya a jihar Filato - Rundunar 'yan sanda

Abinda ke ci mana tuwo a kwarya a jihar Filato - Rundunar 'yan sanda

Rundunar 'yan sanda a jihar Filato ta koka a kan yawaitar sata da kwacen motar jama'a a jihar, tayi kira ga masu motoci da su dauki matakan kare ababen hawansu.

DSP Terna Tyopev, kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Filato, ne ya sanar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar a yau, Litinin, a Jos.

A cewar Tyopev, lamarin satar motar na karuwa ne saboda matsowar bukukuwan 'Easter', saboda masu kwacen na bukatar kudin da zasu yi bushashsa da su lokacin bukukuwan.

"Rundunar 'yan sanda ta lura cewar an samu dawowar yawan aiyukan ta'addanci, musamman kwacen mota a fadin jihar Filato.

"Hakan ba zai rasa nasaba da bukatar kudi da jama'a ke yi ba saboda matsowar bukukuwan 'Easter'.

Abinda ke ci mana tuwo a kwarya a jihar Filato - Rundunar 'yan sanda

Abinda ke ci mana tuwo a kwarya a jihar Filato - Rundunar 'yan sanda
Source: UGC

"Muna bawa masu motoci a fadin jihar nan shawarar da su dauki matakan kare ababen hawansu; ta hanyar saka magarkami a feda ko sitiyari da kuma na'urar gano abu idan ya bata (Tracking devices)," a cewar Tyopev.

Kakakin ya bukaci mazauna jihar da su nemi karin tsaro daga ofishin 'yan sanda ma fi kusa da su yayin bukukuwan 'Easter' domin tabbatar da tsaron lafiyar su da ababen hawansu.

DUBA WANNAN: Harkallar tikiti: EFCC ta kama ma'aikatan tashar jirgin kasa 5 a Kaduna, sunaye

Sannan ya kara da cewa rundunar 'yan sanda ta tashi haikan wajen ganin ta kama masu kwacen motar da aikata sauran miyagun laifuka.

Ya yi kira ga mazauna sassan jihar da su gaggauta sanar da motsin mutanen da basu yarda da su ba ga ofishin 'yan sanda ma fi kusa ko kuma ta hanyar kiran wadannan lambobin waya; 07059473022, 08038907662, 08075391844, and 09053872296.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel