Yanzu Yanzu: An kama daya daga cikin wadanda suka yi fashin bankin Ondo bayan kashe mutum 6 (hoto)

Yanzu Yanzu: An kama daya daga cikin wadanda suka yi fashin bankin Ondo bayan kashe mutum 6 (hoto)

Rundunar sojojin Najeriya a yammacin ranar Litinin, 8 ga watan Afrilu, ta kama daya daga cikin yan fashin da suka kai mamaya wani banki a Idoani, wani gari a jihar Ondo, wanda yayi sanadiyar mutuwar akalla mutum shida.

An tattaro cewa sojoji ne suka kama wanda ake zargin yayinda yake kokarin tserewa daga wajen da fashin ya afku.

Ana zaton mai laifin wani mamba ne a kungiyar mutum 11 da suka kai farmaki banki sannan suka sace makudan kudade.

Yanzu Yanzu: An kama daya daga cikin wadanda suka yi fashin bankin Ondo bayan kashe mutum 6 (hoto)

Yanzu Yanzu: An kama daya daga cikin wadanda suka yi fashin bankin Ondo bayan kashe mutum 6
Source: UGC

Television Continental ta rahoto cewa daga cikin wadanda aka kashe harda wani sufeton dan sanda, ma’aikatan bankin biyu, kwastamomi biyu da suka je cire kudi ta ATM, da kuma wasu mutane biyu a wajen.

Rahoton ya kara da cewa mutum biyar sun ji rauni sannan an kai su asibiti cin gaggawa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari yayi jawabi ga shugabannin duniya a Dubai, ya koka kan amfani da na’urar zamani wajen magudin zabe

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, wasu 'yan fashi da ake yiwa lakabi da 'Daredevil' sun kaddamar da fashi da makami a wani bankin 'yan kasuwa da ke garin Idoani a karamar hukumar Ose da ke jihar Ondo, Kudu maso Yammacin Nigeria.

Bankin, wanda ke ya ke a rukunin gidaje na Isewa, shi ne kadai banki a garin.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel