Matasa sun yi zanga-zanga a Plateau da wasu jihohi, sun nemi a ba arewa ta tsakiya kakakin majalisa

Matasa sun yi zanga-zanga a Plateau da wasu jihohi, sun nemi a ba arewa ta tsakiya kakakin majalisa

Wasu matasa a jihohin Plateau, Niger, Nassarawa sun bukaci a bai wa yankin Arewa ta Tsakiya mukamin kakakin majalisar wakilai.

Matasan sun bayyana bukatan ne a zanga zanga da aka gudanar a ranar Litinin, 8 ga watan Afrilu a jihohinsu.

A jihar Plateau, masu zanga zangan a karkashin kungiyar ‘North-Central Concerned Youths’ sun gudanar da zanga zanga cikin lumana a Jos, inda suke kira da cewa a kai ma yankin mukamin kakakin majalisa don adalci da kuma gaskiya.

Sun hadu ne a ofishin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Jos, dauke da kwalaye masu dauke da rubutu daban daban.

Masu zanga-zangan sun karfafa cewa rawar da yankin Arewa ta Tsakiya ta taka a zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019 na kasa.

Matasa sun yi zanga-zanga a Plateau da wasu jihohi, sun nemi a ba arewa ta tsakiya kakakin majalisa

Matasa sun yi zanga-zanga a Plateau da wasu jihohi, sun nemi a ba arewa ta tsakiya kakakin majalisa
Source: Depositphotos

Haka zalika, sunyi kira ga shugabancin APC da su sa hannu cikin lamarin don tabbatar da cewa ba a bar yankin a baya ba, wajen shugabancin majalisar dokokin kasa.

Zanga zanga makamancin haka ya gudana a Minna, babban birnin jihar Neja inda matasa suka zargi shugabancin jam’iyyar da shirin barin yankin Arewa ta tsakiya a gefe.

Matasan wadanda suka kasance dauke da rubuce rubuce sun bukaci shugaban kasa da ya sanya baki a lamarin don tabbatar da cewa an bi cancanta.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari yayi jawabi ga shugabannin duniya a Dubai, ya koka kan amfani da na’urar zamani wajen magudin zabe

Sun kara da cewa duk yunkuri wajen hana yankin daga tsayar da kakakin majalisa suna hakan ne ba don son ganin hadin kan kasar ba.

Wasu matasan a jihar Nasarawa duk da haka sunyi zanga zanga a titinan Lafia don bukatar ganin an baiwa yankin Arewa ta Tsakiya damar jagorancin majalisan wakilai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel