Rikicin Majalisa: Ya kamata APC ta kori Sanatocin da ke ja da Lawan - Ibrahim

Rikicin Majalisa: Ya kamata APC ta kori Sanatocin da ke ja da Lawan - Ibrahim

Idan har jam’iyyar APC mai mulki tayi amfani da shawarar da Sanata Abu Ibrahim ya ba ta a game da shugabancin majalisa, za ta iya korar Mohammed Ali Ndume da kuma Mohammed Danjuma Goje.

Ko da dai Sanata Abu Ibrahim bai kira sunayen Sanatocin da yake magana a kai ba, ya nemi APC ta fatattaki duk wani Sanatan da yayi kokarin hada-kai da Sanatocin PDP a zaben shugabannin majalisa daga cikin jam’iyyar.

Sanatan na Katsina ta Kudu ya bayyanawa ‘yan jarida a Abuja cewa ya kamata uwar jam’iyyar APC ta dauki mataki mai tsauri na korar wadanda ke kokarin kawo mata matsala wajen nada shugabannin majalisar tarayya.

Abu Ibrahim yayi wannan bayani ne a Ranar Lahadi, 7 ga Watan Afrilun 2019 inda yace dole duk wani ‘dan siyasar da ya shigo cikin jam’iyyar APC ya amince da matakin da uwar jam’iyyar ta dauka idan yana so a tafi da shi.

KU KARANTA: Sabon Sanatan APC ya ba Uwar Jam’iyya shawara kan rikicin Majalisa

Rikicin Majalisa: Ya kamata APC ta kori Sanatocin da ke ja da Lawan - Ibrahim

APC tayi ma kowa riga da wando don haka dole ayi biyayya – Abu Ibrahim
Source: Facebook

A halin yanzu dai irin su Sanata Mohammed Ali Ndume su na da nufin tsayawa takarar shugaban majalisar dattawa, duk da cewa jam’iyyar APC ta tsaida Ahmad Lawan a matsayin wanda ta ke so ya gaji Bukola Saraki a majalisar tarayya.

Sanata Ibrahim yana ganin cewa babban laifi ne yin fito-na-fito da matakin da jam’iyya ta dauka na zakulo wanda zai rike majalisar. Sanatan yake cewa aikin jam’iyya ne ta fitar da wadanda za su ja ragamar majalisa dattawa a kasar.

Babban ‘Dan majalisar yake cewa PDP ba za ta samu irin damar da ta samu a 2015 ba inda ya kara da cewa tun da jam’iyya ke bada tikiti, ya zama dole ayi mata biyayya a duk matakin da ta dauka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel