Kara kudin tikiti: EFCC ta kama ma'aikatan tashar jirgin kasa 5 a Kaduna, sunaye

Kara kudin tikiti: EFCC ta kama ma'aikatan tashar jirgin kasa 5 a Kaduna, sunaye

Hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ta kama wasu ma'aikatan hukumar kula da tashar jirgin kasa na Kaduna saboda harkallar kudin tikitin jirgi zuwa Abuja.

Idan baku manta ba, Legit.ng ta wallafa wani rahoto a kan yadda matafiya ke cigaba da cika tasahar jiragen kasa a Abuja da Kaduna, duk da hobbasa da shugaban rundunar 'yan sanda (IGP), Mohammed Adamu, ya yi wajen kafa wata rundunar atisaye ta musamman da aka yiwa da 'Operation Puff Adder', a ranar Juma'a, domin magance satar mutane da hana aiyukan ta'addanci a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Matafiya sun cika a tsahar jirgin kasa ta Idu a Abuja da ta Rigasa a Kaduna da duku-dukun ranar Asabar domin samun damar yankan tikitin jirgi.

Kara kudin tikiti: EFCC ta kama ma'aikatan tashar jirgin kasa 5 a Abuja, sunaye

EFCC ta kama ma'aikatan tashar jirgin kasa 5 a Abuja
Source: Twitter

Yawaitar fasinjoji a tashar jiragen kasa ta haddasa wahakar tikitin jirgi. Hakan ya sa wasu daga cikin ma'aikatan tasahar jiragen boye tikiti tare da kara masa farashi fiye da kima.

DUBA WANNAN: Abinda yasa hana hakar gwal ba zai magance rikicin Zamfara ba - Shehu Sani

Binciken manema labarai ya gano cewar ma'aikatan kan ayar da tikitin jirgi da suka boye a kan farashin N3,000 zuwa N5,000.

Ma'aikatan biyar da EFCC ta kama sune; Clement Zakka,, Udim Sunday Samson, Adams Danladi, Otitomoni Omobolanle da Hassan Dauda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel