Yanzu yanzu: Yan fashi sun kai sumame wani banki a Ondo

Yanzu yanzu: Yan fashi sun kai sumame wani banki a Ondo

Rahotannin da muke samu yanzu na nuni da cewa wasu 'yan fashi da ake yiwa lakabi da 'Daredevil' sun kaddamar da fashi da makami a wani bankin 'yan kasuwa da ke garin Idoani a karamar hukumar Ose da ke jihar Ondo, Kudu maso Yammacin Nigeria.

Bankin, wanda ke ya ke a rukunin gidaje na Isewa, shi ne kadai banki a garin.

KARANTA WANNAN: Onnoghen ya yi murabus: PDP na cike da kunya - BMO

Wakilin TVC, Ayodeji Moradeyo ya ruwaito cewa 'yan fashin na gudanar da fashi da makamin a dai-dai wannan lokaci dauke da muggan makamai.

Rahotanni sun bayyana cewa sun samu damar shiga bankin ne ta hanyar amfani da wani abun fashewa.

Cikakken labarin yana zuwa...

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel