Bayan ganawarsa da Osinbajo, Ndume ya yi nuni da cewa ba zai janye ba

Bayan ganawarsa da Osinbajo, Ndume ya yi nuni da cewa ba zai janye ba

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, a ranar Litinin ya yi ganawar sirri da tsohon shugaban masu rinjaye a majalisa, Ali Ndume, wanda ke neman kujerar shugaban majalisar dattawa a zaben da za'a gudanar a watan Yuni, 2019.

Ya alanta niyyar takararsa duk da cewa jam'iyyarsa ta All Progressives Congress APC ta bayyana wanda take goyon baya a matsayin Sanata Ahmad Lawan.

Ndume ya ki magana da manema labaran fadar shugaban kasa bayan ganawarsa na tsawon sa'a daya da mataimakin shugaban kasar amma ya yi nuni da cewa ba zai janye daga takarar ba.

Yayinda manema labaran suka tambayesa shin zai janye, yace : "Ni? .., yanzu ba lokacin magana bane saboda ina cigaba da neman shawarwari."

Mun kawo muku rahoton cewa Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo a ranar Litinin, 8 ga watan Afrilu ya yi ganawar sirri da tsohon Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume.

Sun fara ganawar da misalin karfe 3:20 na rana lokacin da Ndume ya isa ofishin mataimakin Shugaban kasa.

Ndume na ta zawarcin kujerar Shugaban majalisar dattawa na tara wanda za a rantsar a watan Yuni.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel