Onnoghen ya yi murabus: PDP na cike da kunya - BMO

Onnoghen ya yi murabus: PDP na cike da kunya - BMO

- Kungiyar BMO ta ccaccaki jam'iyyar adawa ta PDP akan goyon bayan da suka nunawa tsohon alkalin alkalai na kasa

- Kungyar ta ce abun dariya ne ganin yadda PDP da 'yan korensu suka tsaya tsayin daka akan goyon bayan Onnoghen wanda ake zarginsa da rashawa

- Ta ce ya kamata a ce wasu bangare na al'ummar Nigeria sun fito sun roki afuwar shugaba Buhari akan zarginsa da kuma aibata shi don ya dakatar da Onnoghen

Kungiyar BMO da ke kare muradun shugaban kasa Muhammadu Buhari a kafafen watsa labarai na zamani ta ccaccaki jam'iyyar adawa ta PDP akan goyon bayan da suka nunawa tsohon alkalin alkalai na kasa, tana mai baiwa shuwagabannin jam'aiyyar shawara akan su rufe fuskokinsu don kunya tunda dai yanzu Onnoghen ya yi murabus da kansa akan zargin rashawa da ake yi masa.

A cikin wata sanarwa daga kodinetan kungiyar, Niyi Akinsiju da kuma sakatarenta, Cassidy Madueke, kungyar ta ce abun dariya ne ganin yadda shuwagabannin PDP da 'yan korensu suka tsaya tsayin daka akan goyon bayan mai shari'a Onnoghen wanda ake zarginsa da boye wasu kadarori da kudade masu yawa.

Ya ce murabus din tsohon alkalin alkalan ya tabbatar da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bi ra'asyin kasa wajen dakatar da tsohon alkalan, yana mai cewa "A yanzu 'yan Nigeria sun ga irin dabi'ar shuwagabannin PDP da mambobinsu, da suka hada da tsohon shugaban kasa Atiku Abubakar, wanda ya kai gwauro ya kai mari domin ganin ya kare mai shari'a Onnoghen.

KARANTA WANNAN: Yadda aka ci mutuncin mata a zaben 2019 - Yan takara mata

Mai shari'a Walter Onnoghen

Mai shari'a Walter Onnoghen
Source: UGC

"Shuwagabannin jam'iyyar sun dakatar da yakin zabensu na shugaban kasa a wancan lokacin har na tsawon awanni 72! Kawai saboda goyawa rashin gaskiya baya, amma zuwa yanzu 'yan Nigeria sun san cewa karya fure take bata 'yaya.

"Ba mu yi mamaki ba, da muka ga wani kusa a jam'iyyar PDP, shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki, ya so ya sanya majalisar cikin lamarin shari'ar Onnoghen, har sai da jiga jigan APC wadanda suke da mafi rinjaye suka dakile hakan.

"Ba zamu kuma manta yadda gwamnonin PDP daga Kudu maso Kudu suka huro wuta ba, musamman ta yadda suka bukaci mutumin da ake kallo a matsayin ginshikin shari'a na kasar da kar ya gurfana gaban kotun ladabtar da ma'aikata (CCT).

"Amma a yanzu da Onnoghen ya yanke hukuncin da tun tuni ya kamata ya yanke, hakan ya bayyana halayen shuwagabannin PDP karara, na son rashin gaskiya, da daurewa karya gindi. Dukkanin wadannan abubuwan da suka faru, sun tabbatar da cewa PDP jam'iyya ce da ke goyon bayan masu cin hanci da rashawa."

A cewarsu, ya kamata a ce wasu bangare na al'ummar Nigeria sun fito sun roki afuwar shugaban kasa Muhammadu Buhari akan zarginsa da kuma aibata shi don ya dakatar da mai shari'a Onnoghen, kuma bisa dogaro da umurni daga kotun CCT.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel