Ba mu nemi mu ci zabe da karfi da yaji ba kamar yadda PDP su ka saba inji APC

Ba mu nemi mu ci zabe da karfi da yaji ba kamar yadda PDP su ka saba inji APC

Babban Sakataren yada labarai na kasa na APC, Lanre Issa-Onilu, ya bayyana cewa rashin bin irin hanyar da jam’iyyar PDP ta saba na cin zabe ko ta karfin tsiya ya sa ta rasa wasu jihohi a zaben 2019.

Babban jigon na na jam’iyyar APC mai mulki yake cewa ba su bari sun yi amfani da hanyar cin zabe ta karfi da yaji ba a jihohin da ta rasa gwamnonin ta. Issa-Onilu ya bayyana wannan ne a wata hira da yayi da ‘Yan jarida a Abuja.

Malam Issa-Onilu yake cewa abin mamaki ne ace jam’iyyar da ke rike da madafan iko ta rasa jihohin da ke hannun ta. Onilu yace APC ba ta nemi tayi karfa-karfa a zaben gwamnoni na jihohin Imo, Adamawa, Bauchi da kuma Oyo ba.

KU KARANTA: Oshiomhole bai isa ya shiga maganar Majalisa ba – Sanatan PDP

Ba mu nemi mu ci zabe da karfi da yaji ba kamar yadda PDP su ka saba inji APC

Isa Onilu yace APC tace ba ta nemi cin zabe ta kowane irin hali ba
Source: Facebook

Mai magana da yawun jam’iyyar yake cewa gwamnatin APC ta bada damar da ake bukata domin ganin kowa ya zabi wanda yake so. Issa Onilu yake cewa abin da aka san PDP da shi, shi ne ta ci zabe da karfin tsiya har a tafi gaban kotu.

Jam’iyyar tayi tsokaci a kan zaben jihar Oyo da Akwa-Ibom, inda gwamnan jihar Oyo ya gaza samun ko da kashi 1/3 na kuri’un da yake bukata domin ya lashe zaben Sanata. A Akwa-Ibom kuma, Sanata Godswill Akpabio ya sha kasa.

Kakakin na APC yake cewa sun rasa babban zaben da aka yi a jihohin Oyo da Ondo duk da cewa su ke da gwamnoni a yankin. Issa Onilu yace an kyale mutane sun yi zaben su a bana ba tare da murdiya ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel