Abinda yasa hana hakar gwal ba zai magance rikicin Zamfara ba - Shehu Sani

Abinda yasa hana hakar gwal ba zai magance rikicin Zamfara ba - Shehu Sani

Shehu Sani, sanatan jihar Kaduna ta tsakiya, ya bayyana ra'ayinsa a kan dakatar da hakar gwal da gwamnatin tarayya tayi a jihar Zamfara saboda dalilan tsaro.

A ranar Lahadi ne gwamnatin tarayya, ta bakin shugaban rundunar 'yan sanda (IGP), Adamu Mohammed, ta sanar da dakatar da hakar tare da yin barazanar kwace lasisin duk wanda bai yi biyayya ga umarnin ba.

Kazalika, gwamnatin tarayya ta bawa bakin haure umarnin barin yankin cikin sa'a 48 domin samun damar yaki da 'yan bindiga da suka hana jihar zama lafiya

Da yake bayyana ra'ayinsa a shafinsa na tuwita, Shehu Sani, ya yaba wa gwamnatin tarayya bisa daukan matakin.

Abinda yasa hana hakar gwal ba zai magance rikicin Zamfara ba

Shehu Sani
Source: Twitter

Sai dai, Sani ya bayyana cewar dakatar da hakar gwal a Zamfara ba shine zai kawo karshen aiyukan ta'addanci a jihar ba.

DUBA WANNAN: Na san manyan arewa da ke da hannu a kisan rayuka a Zamfara - Sheikh Abdallah Gadon Kaya

A cewar sa; "dakatar da hakar ma'adanai a Zamfara abu ne me kyau, amma hakan ba zai kawo karshen aiyukan ta'addanci a jihar ba.

"Muna cikin yaki ne, kuma abinda ya fi kamata ga gwamnati a irin wannan lokaci shine ta tashi haikan domin kare jama'ar ta."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel