Shugabancin majalisa: Sanata Lawan na da cikakken goyon bayan mutane da dama - Kungiya

Shugabancin majalisa: Sanata Lawan na da cikakken goyon bayan mutane da dama - Kungiya

Wata Kungiyar siyasa mai suna Sustainable Democracy Agenda (SUDA), ta ce dan takaran kujerar Shugaban majalisar dattawa a jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Sanata Ahmed Lawan na tare da goyon bayan manyan mutane da dama.

Jagoran kungiyar SUDA, Ibrahim Usman, ya bayyana hakan a jawabin da aka bayyanawa manema labarai a ranar Litinin a Abuja.

Usman yace sakamakon binciken da kungiyar ta gudanar a fadin kasar, ya bayyana cewa Lawan ya samu goyon bayan yawancin yan Najeriya a yunkurinsa na neman kujeran Shugaban majalisa.

A cewar shi, sakamakon gwajin da Kungiyar SUDA ta gabatar, ya nuna cewa kashi 75 na kuri’u sun kasance na Sanata Lawan.

Shugabancin majalisa: Sanata Lawan na da cikakken goyon bayan mutane da dama - Kungiya
Shugabancin majalisa: Sanata Lawan na da cikakken goyon bayan mutane da dama - Kungiya
Source: UGC

Ya cigaba da cewa kashi 12.5 sun goyi bayan Sanata Goje, 9.8% kuma sun goyi bayan Ndume, sannan kashi 2.5 da suka rage basu yanke shawara ba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Osinbajo da Ndume na cikin ganawa a Aso Rock

Usman ya jera sunayen yan takaran a matsayin sanata Lawan, Sanata Mohammed Danjuma Goje da kuma Sanata Mohammed Ali Ndume.

Jagoran shirin yace gwajin ya nuna cewa zabin Lawan bai zamo tursasawa ba daga shugabancin APC kamar yanda wadanda ke adawa da lamarin ke ikirari.

A cewar shi, shawara ce da ke nuna goyon bayan yawancin yan Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Online view pixel