Yanzu-yanzu: Gobara a babban filin jirgin sama (Bidiyo)

Yanzu-yanzu: Gobara a babban filin jirgin sama (Bidiyo)

Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa gobara ya tashi a babban filin jirgin saman Sam Mbakwe dake birnin Owerri, jihar Imo ranar Litinin, 8 ga watan Afrilu, 2019 inda fasinjoji suke neman mafaka.

Da farko ba'a san abinda ya sabbab gobaran ba amma daga baya wata majiya ta bayyanawa manema labarai cewa wasu gyare-gyare da ake a bangaren masu sauka ne ya sabbaba gobarar.

An tattaro cewa gobarar ta fara misalin karfe 2:10 na rana kuma ta kwashe mintuna 50 tana ci bal-bal. Sai lokacin da jami'an hukumar kwana-kwana sun kawo agaji aka samu kashe wutan.

Majiyar tace: "Abun ya faru a sashen masu sauka na filin jirgin sama inda ake gyara. Da abun ya fi haka amma zuwa jami'an kwana-kwana ya tsagaita abin."

"Gobarar ta fara misalin karfe 2:10 na rana kuma an kwashe mintuna 50. Ta lalata kayayyakin aiki amma an takaita abin."

Yanzu-yanzu: Gobara a babban filin jirgin sama (Bidiyo)

Yanzu-yanzu: Gobara a babban filin jirgin sama (Bidiyo)
Source: Facebook

Yanzu-yanzu: Gobara a babban filin jirgin sama (Bidiyo)

Yanzu-yanzu: Gobara a babban filin jirgin sama (Bidiyo)
Source: Facebook

Ku saurari cikakken rahoton....

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel