Yanzu Yanzu: Osinbajo da Ndume na cikin ganawa a Aso Rock

Yanzu Yanzu: Osinbajo da Ndume na cikin ganawa a Aso Rock

Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo a ranar Litinin, 8 ga watan Afrilu ya yi ganawar sirri da tsohon Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume.

Sun fara ganawar da misalin karfe 3:20 na rana lokacin da Ndume ya isa ofishin mataimakin Shugaban kasa.

Ndume na ta zawarcin kujerar Shugaban majalisar dattawa na tara wanda za a rantsar a watan Yuni.

Ya kaddamar da kudirinsa na neman takarar kujerar shugabancin majalisar duk da tsayar da Shugaban masu rinjaye a majalisa mai ci, Ahmed Lawan da fadar Shugaban kasa da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) suka yi.

Yanzu Yanzu: Osinbajo da Ndume na cikin ganawa a Aso Rock
Yanzu Yanzu: Osinbajo da Ndume na cikin ganawa a Aso Rock
Source: UGC

Har yanzu Osinbajo da sanatan na kan ganawa a daidai lokacin wannan rahoton.

KU KARANTA KUMA: Cin bashi a kasashen ketare: Kaduna, Legas, Edo da Cross River sun ciri tuta

A baya Legit.ng ta rahoto cewa wata gamayyar kungyoyin damokradiyya ta bukaci Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da fadar shugaban kasa da su kiyayi kura-kurai irin na baya su kuma guji tursasa shuwagabanni a majalisar dokokin kasa, musamman majalisan dattijai.

Kungiyar tayi gargadin cewa yunkurin da gwamnatin baya tayi wajen dora shuwagabannin majalisar dokoki, ya kan zo da rashin jituwa daga karshe har da tsige wadanda fadar shugaban kasar ta dora, inda ta ba da misali akan lamari irin haka a gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Online view pixel