Yanzu-yanzu: Idris Wase ya janyewa Femi Gbajabiamila

Yanzu-yanzu: Idris Wase ya janyewa Femi Gbajabiamila

Rahoto da majiya mai karfi ya nuna cewa dan majalisar wakilan tarayya, Hanarabul Idris Wase ya amince da janyewa shugaban masu rinjaye, Hanarabul Femi Gbajabiamila, daga takarar kujeran kakakin majalisar wakilan tarayya na tara.

Wannan abu ya bayyana ne yayinda wani dan majalisar Hanarabul Dyegh, wanda shine dirakta janar na yakin neman zaben Sadiq Wase ya alanta takarar kujeran.

Wadanda suka bayyana niyyar takarar kujeran kawo yanzu sune Hon. Femi Gbajabiamila (APC, Lagos), Hon. Umaru Mohammed Bago (APC, Niger) da Hon. Nkeiruika Onyeojocha (APC, Abia).

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Kotun Koli ta yi watsi da karar Sanata Magnus Abe kan zaben fidda gwanin APC

Wani mamban yan majalisan APC na yankin Arewa maso tsakiya ya bayyanawa jaridar New Telegraph cewa "Wase ya yaudaremu ta hanyar yanjewa daga takarar a boye da kuma marawa Hanarabul Gbajabiamila baya saboda ya samu kujerar mataimakin kakaki."

Yan majalisa daga yankin Arewa maso tsakiya mun yi yarjejeniyar cewa za mu nemi kujeran kakakin majalisa kuma mun kasance muna yiwa Wase aiki, amma sai aka kirashi fadar shugaban kasa kuma ya amince da kujeran mataimakin kakaki."

"Bai sanar da mu ba; ya boye mana kuma hakan yasa wajibi ne mu nemi mafita. An yiwa John Dyegh tayin kujeran mataimakin kakaki kafinsa amma bai amsa ba saboda manufar yankin."

"Amma Wase, wanda muka kasance mun yiwa aiki; ba zamu sake yarda da shi ba."

Karin bayani kan gayyatar da aka yiwa Wase fadar shugaban kasa, an bayyana cewa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i; gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello; da gwamnan jihar Nasarawa, Tanko Al-Makura, suka zannan da shi har ya amince.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel