Yarimomi 15 na zawarcin kujerar Etsu Patigi

Yarimomi 15 na zawarcin kujerar Etsu Patigi

- Yarimomi 15 a masarautan karamar hukumar Patigi ne suka bayyana ra’ayin su na son zama sabon Etsu Patigi, bayan mutuwar Etsu Patigi Alhaji Ibrahim Chatta-Umar

- Sun fara zawarcin ne a ma'aikatar kananan hukumomi da harkokin masarauta na jihar

- Kwamishinan ma’aikatar yace tuni an tura sunayen wadanda suka bayyana ra’ayoyin su ga majalisar masu nadi don tantancewa

Akalla Yarimomi 15 masu jiran gado a masarautan karamar hukumar Patigi ne suka bayyana ra’ayin su na son zama sabon Etsu Patigi, bayan mutuwar Etsu Patigi Alhaji Ibrahim Chatta-Umar kwanan nan.

Alhaji Saheed Habeeb, kwamishinan kananan hukumomi da harkokin masarauta na jihar ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Illorin a ranar Litinin, 8 ga watan Afrilu.

Habeen ya bayyana cewa masu hamayya 15 wadanda suka kasance daga kabilu daban-daban a Patigi sun gabatar da rokonsu ga ma’aikatar.

Yarimomi 15 na zawarcin kujerar Etsu Patigi
Yarimomi 15 na zawarcin kujerar Etsu Patigi
Source: UGC

Ya ci gaba da cewa ma’aikatar har ila yau tana kan karban roko.

Kwamishinan ya ce ma’aikatar ta tura sunayen wadanda suka bayyana ra’ayoyin su ga majalisar masu nadi don tantancewa.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar RIPAN tace an shigo da buhuhunan shinkafa sama da miliyan 20 cikin wata 3 kacal

NAN ta rahoto cewa basaraken wanda ya kasance mataimakin shugaban majalisar sarakunan jihar Kwara, ya mutu a ranar 20, yana kuma da shekaru 69.

Ya kasance tsohon babban akanta, ya shugabanci masarautar har na tsawon shekaru 19 da watanni 10.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Online view pixel