Bankin Musulunci ta Duniya ta baiwa Najeriya tallafin N186,000,000 domin aikin Hajji

Bankin Musulunci ta Duniya ta baiwa Najeriya tallafin N186,000,000 domin aikin Hajji

Gwamnatin tarayya ta rattafa hannu akan wata yarjejeniyar samun tallafin dala dubu dari biyar da ashirin da uku da dari takwas da ashirin da uku ($523,823), kimanin naira miliyan dari da tamanin da shida kenan (N186,000,000) daga babban bankin Musulunci na Duniya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito an kulla wannan yarjejeniya ne a birnin Marrakesh na kasar Morocco a yayin taron babban bankin na 44, inda ministar kudi, Zainab Ahmed ta rattafa hannu a madadin Najeriya, yayin da shugaban bankin, Bandar Hajjar ya rattafa hannu a madadin Bankin.

KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da yaron wani babban dan siyasa a Abuja

A jawabinta, Minista Zainab ta bayyana cewa za ayi amfani da wadannan kudade ne wajen horas da jami’an hukumar kula da aikin Hajji ta Najeriya, tare sayen ma hukumar duk wasu kayan aiki da take bukata, da kuma gyaran wasu kayan aikin.

Haka zalika tace gwamnatin Najeriya za tayi amfani da wani kaso na kudin wajen gudanar da aikin habbaka sha’anin kamfanunuwan sarrafa auduga wajen hada kayan sawa a Najeriya ta ma’aikatan ciniki, kasuwanci da zuba jari.

Da take bayyana yadda za’a raba kudaden, Minista Zainab Shamsuna Ahmad ta bayyana cewa hukumar kula da aikin Hajji ta kasa zata samu dala dubu dari biyu da arba’in da uku da dari takwas da ashirin da uku ($243,823) yayin da ma’aikatan ciniki zata samu $280,000.

Daga karshe jawabinta, Ministar ta bayyana ma mahalarta taron cewa gwamnonin jahohin Najeriya na iya bakin kokarinsu wajen inganta harkar noma a jahohinsu ta hanyar amfani da kungiyoyin manoma, ta yadda suke basu bashin jarin noma ba tare da neman jingine wani abu ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel