An dambace tsakanin Kansiloli da shugaban karamar hukuma akan N300,000

An dambace tsakanin Kansiloli da shugaban karamar hukuma akan N300,000

Rai ya dugunzuma, an kuma kai hankali nesa a karamar hukumar Oshimili ta kudu jahar Delta, inda aka dambace tsakanin shugaban karamar hukumar, Mista Uche Osadebe da kansilolinsa akan zarginsa da suke yi da wawuran kudin yakin neman zabe da gwamnan jahar, Ifeanyi Okowa ya bayar.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito guda daga cikin daraktocin karamar hukumar ya bayyana cewa rikici ya fara tasowa ne yayin da ake saura kwanaki uku da zabe, lokacin da kansilolin suka nemi Ciyaman ya basu rabonsu daga kudin zaben da gwamnan ya baiwa karamar hukumar.

KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da yaron wani babban dan siyasa a Abuja

An dambace tsakanin Kansiloli da shugaban karamar hukuma akan N300,000

Jama'an karamar hukumar Oshimili
Source: UGC

Sai dai Ciyaman Osadebe ya fara musu kame kame, har ma ya bayyana musu cewa ai ya baiwa shugaban majalisar kansilolin naira dubu dari uku (N300,000), hakan ne ya harzuka kansilolin, inda suka afka cikin ofishinsa bayan sun tattara kansu, suka lakada masa dan banzan duka.

“Sakatariyar karamar hukumar ta zamto tamkar filin daga, inda aka hangi jama’a suna ta kai ma junansu naushi babu ko kakkautawa, da kyar da sudin goshin jami’an Yansanda suka shiga tsakani, sa’annan suka kama Ciyaman da kansilolin.

“Ba’a tsaya ko ina ba sai ofishin DPO, CSP Ukang Esther dake kula da karamar hukumar, itace ta shawo kan lamarin, tare da warware matsalar.” Kamar yadda darakta a karamar hukumar ya bayyana.

Dama dai kansilolin sun dade suna kule da Ciyaman Osadebe tun lokacin da karamar hukumar ta samu tallafin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya raba ma jahohi don biyan bashi, inda suke zarginsa da cinye naira miliyan 10 daga cikin kudade.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel