Yanzu-yanzu: Kotun Koli ta yi watsi da karar Sanata Magnus Abe kan zaben fidda gwanin APC

Yanzu-yanzu: Kotun Koli ta yi watsi da karar Sanata Magnus Abe kan zaben fidda gwanin APC

Kotu kolin Najeriya ta yi watsi da karar da Sanata Magnus Abe ya shigar kan zaben fidda gwanin gwamnan jam'iyyar All Progressives Congress APC a jihar Ribas da aka gudanar a shekarar 2018.

Wannan na faruwa ne bayan kotun daukaka kara ta haramtawa jam'iyyar APC musharaka a zaben 2019 da kuma umurtan hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta watau INEC cewa kada ta sanya APC a takardar kuri'a.

Bayan kammala zaben da APC batayi musharaka ba, dukkanin alkalai kotun kolin karkashin jagorancin mukaddashin shugaban Alkalan Najeriya, Tanko Muhammad, sun yi ittifakin cewa karar Magnus Abe shirme ce.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Kotun Koli ta yi watsi da karar Sanata Magnus Abe kan zaben fidda

Za ku tuna cewa a ranar 7 ga watan Junariu, babban kotun tarayya dake zaune a PortHarcourt ta yi watsi da dukkan sakamakon zaben fidda gwanin da bangarorin jam'iyyar APC biyu suka gudanar a jihar.

Alkali Kolawale Omotosho, wanda ya yanke shari'ar ya hana hukumar INEC sanya sunayen Tonye Cole na bangaren Amaechi da Magnus Abe wanda yayiwa jam'iyyar tawaye a takardar kuri'a.

Ya ce dukkaninsu basu gudanar da zaben fidda gwanin bisa ga doka ba kuma INEC ta saba doka wajen sanya sunansu tun daga farko dubi ga umurin da kotu ta bada a baya.

Sakamakon haka Sanata Abe ya shigar da kara kotun koli domin ta tabbatar da zaben da ya samu nasara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel