Kungiyar RIPAN tace an shigo da buhuhunan shinkafa sama da miliyan 20 cikin wata 3 kacal

Kungiyar RIPAN tace an shigo da buhuhunan shinkafa sama da miliyan 20 cikin wata 3 kacal

Kungiyar masu casar shinkafa ta Najeriya (RIPAN), ta koka kan cewa a cikin watanni uku kacal da suka gabata, an yi fasa kwaurin shinkafa sama da miliyan 20 cikin kasar nan.

Shugaban RIPAN, Mohammed Maifata ne ya bayyana haka a yayinda ya ke wa manema labarai bayani a Abuja, dangane ya yawaitar shigo da shinkafa a cikin kasar nan, duk kuwa da cewa gwamnatin tarayya ta haramta shigo da ita.

Ya kuma nuna takaicin cewa yayin da milyoyin ‘yan Najeriya suka zuba jari a cikin kasar nan wajen inganta noma da cashe shinkafa, abin bakin ciki shi ne yadda a cikin watanni uku kadai aka shigo da sama da metric tan na shinkafa har milyan daya.

Kungiyar RIPAN tace an shigo da buhunan shinkafa sama da miliyan 20 cikin wata 3 kacal

Kungiyar RIPAN tace an shigo da buhunan shinkafa sama da miliyan 20 cikin wata 3 kacal
Source: Depositphotos

Ya ce ya na daidai da buhu milyan 20 kenan mai cin Kg 50.

Ya kara da cewa masu sumogal na karya kanana da manyan manoman shinkafa, kuma su na janyo wa Najeriya asarar bilyoyin kudade zuwa kasashen waje, tare kuma da asarar kudaden shiga cikin kasa.

KU KARANTA KUMA: Mun bi tsare-tsaren da ya kamata kafin hukunta yar Najeriya - Saudiyya

Ya ce abin mamaki ne duk da irin matakan tsaron da ake sa wa, amma kan iyakokin Najeriya sun koma dandalin safarar shinkafa sannan kasuwannin cikin kasa cike suke makil da shinkafar da ake sumogal daga kasashen waje.

Ya ce wannan matsala za ta gurgunta shirin noman shinkafa a kasar nan, sannan kuma ta kassara kanana da manayan manoman shinkafa da masu kasuwancin ta a cikin kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel