Kada ku tursasa wa majalisar dokoki shugabanni – Magoya bayan Ndume ga APC

Kada ku tursasa wa majalisar dokoki shugabanni – Magoya bayan Ndume ga APC

- Wata gamayyar kungyoyin damokradiyya ta bukaci Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da fadar Shugaban kasa da kada su yi kuskuren tursasa shugabanni a majalisar dokokin kasar

- Kungiyar tayi gargadin cewa duk yunkurin da gwamnatocin baya ke yi wajen tursasa shugabanni baya karewa da dadi

- Sun nuna yakinin cewa idan aka bari jagoransu, Sanata Ndume ya zamo Shugaban majalisar dattawa toh babu makawa za a samu alaka mai kyau tsakanin majalisar dokoki da na zartarwa

Wata gamayyar kungyoyin damokradiyya ta bukaci Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da fadar shugaban kasa da su kiyayi kura-kurai irin na baya su kuma guji tursasa shuwagabanni a majalisar dokokin kasa, musamman majalisan dattijai.

Kungiyar tayi gargadin cewa yunkurin da gwamnatin baya tayi wajen dora shuwagabannin majalisar dokoki, ya kan zo da rashin jituwa daga karshe har da tsige wadanda fadar shugaban kasar ta dora, inda ta ba da misali akan lamari irin haka a gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Babban jagoran kungiyar, Ambasada Auwal Alhassan Gama ya fada ma taron manema labarai a ranar Litinin a Abuja, cewa gwamma a baiwa yan majalisan da ake dauka a matsayin masu aminci su zabi wadanda za su shuwagabance su.

Kada ku tursasa wa majalisar dokoki shugabanni – Magoya bayan Ndume ga APC

Kada ku tursasa wa majalisar dokoki shugabanni – Magoya bayan Ndume ga APC
Source: UGC

Sun nuna yakinin cewa idan aka basu damar zaban shuwagabannin su, Sanata Mohammed Ali Ndume zai tsaya a matsayin shugaban majalisan dattijai idan aka yi la’akari da kwarewarsa a matsayin dan majalisa kuma zai tabbatar da kyakkyawar dangantaka tsakanin majalisar zartarwa da majalisar dokoki.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar RIPAN tace an shigo da buhuhunan shinkafa sama da miliyan 20 cikin wata 3 kacal

Kan tambayan ko wani dalili yasa suka fi mayar da hankali ga matsayin shugaban majalisa sannan ba tare da mai da hankali ga matsayin kakakin majalisar wakilai wanda ba a ba ko wani yanki ba, Gama yace sun yanke shawaran yin magana akan matsayin shugaban majalisan dattijai tunda jam’iyyar ta bayyana matsayarta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Online view pixel