An tsare wani dan shekara 40 kan laifin lalata yaro dan shekara 15

An tsare wani dan shekara 40 kan laifin lalata yaro dan shekara 15

Wata kotun majistare da Ogba a Lagas ta tsare wani mutum dan shekara 40, Sulaimon Musa, bisa zargin yin luwadi da dan makwabcinsa.

Yan sanda sun fada ma kotu cewa Musa ya dade yana luwadi da matashin yaron ta duburansa a gidansu da ke unguwarsu ta Baale, Ajegunle, Lagas, tun yaron na dan shekara 11 a duniya.

Dan sandan mai kara, Sufeto Benson Emerhi, yace wani da ke sanya ido ne ya janyo hankalin iyayen yaron duba ga irin kusancin da ke tsakanin yaron da mai laifin.

Emerhi yace Musa ya gargadi yaron akan kada ya sanar da iyayensa a lokacin da ya fara luwadi dashi. Lokacin da yaron, yayi korafin radadin da ya ji a duburansa bayan lamarin, sai mai laifin ya siyo mai wasu kyaututtuka.

An tsare wani dan shekara 40 kan laifin lalata yaro dan shekara 15

An tsare wani dan shekara 40 kan laifin lalata yaro dan shekara 15
Source: Depositphotos

Yace asirin mutumin ya tonu ne a ranar Litinn da ya gabata, lokacin da yaron ya fito daga dakin Musa bayan iyayensa sun yi ta nemansa.

“Iyayen yaron sun tunkare shi sannan ta tona asiri. Da aka yi bincike, an gano cewa duburan yaron ya sauya sakamakon Tarawa da mutumin ke yi dashi ta wajen. An kai rahoton lamarin ga yan sanda sannan aka kama Musa. Daga bisani aka tura lamarin ga sashin kare yanci domin bincike.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Sule Lamido da dansa sun nemi kotu ta saki fasfot dinsu

An shigar da karar mutumin kotu akan tuhume-tuhume biyu na lalata da kuma luwadi.

Kotun ta ki amsa rokonsa bayan Sufeto Emerhi ya nemi kotu ta tura takardarsa ga sashin hukunci na Lagas don jin shawara.

Mai shari’a, Misis O. Sule Amzat, tayi umurnin garkame shi a gidan kurkuku ba tare da beli ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel