Jami'an yan sanda sun kashe yan bindiga 3, sun yi rashin hafsoshi 2

Jami'an yan sanda sun kashe yan bindiga 3, sun yi rashin hafsoshi 2

Hukumar yan sandan jihar Kaduna ta sanar da cewa jami'anta sun hallaka wasu yan bindiga uku da suka kai mumunan hari kauyen Kakangi dake karamar hukumar birnin gwari ranar Asabar, 6 ga watan Afrilu, 2019.

Kakakin hukumar, Yakubu Sabo, ya kara da cewa an yi rashin wasu hafsoshi biyu sakamakon artabu da akayi tsakanin yan bindigan da jami'an yan sanda.

Yan bindiga sun far ma mazauna garin ne yayinda ake gudanar bikin daurin aure a ranar.

Yakubu Sabo ya bayyana sunayen yan sanda suka rigamu gidan gaskiya; Sifeto Aliyu Muhammad, da Sajen Rabiu Abubakar, dukkansu daga ofishin hukumar dake Randagi.

Ya ce wasu sun jikkata wanda ya kunshi Sajen Ibrahim Nasir da suka masu farar hula shida kuma an garzaya dasu babban asibitin dake cikin garin Birnin-gwari.

KU KARANTA: Idris Wase ya janyewa Femi Gbajabiamila

Yace: "Mun samu kira daga Randaji ranar Asabar, 6 ga watan Afrilu 2019 misalin karfe 7 na dare cewa wata ayarin yan bindiga ta shiga kauyen Kakangi dake Birnin-Gwari kusa jihar Neja kuma suka fara harbin kan mai uwa da wabi."

"Da wuri jami'an yan sanda, yan banga suka dira garin kuma aka shiga musayar wuta da yan bindigan inda aka kawar da su."

"Jami'anmu sun hallaka biyu daga cikinsu amma sauran sun arce cikin daji da raunuka. Amma kash! biyu daga cikin jarumanmu sun rigamu gidan gaskiya yayi musayar wuta da yan bindigan."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel