Mutane 11 sun hallaka, 43 sun jikkata sakamakon harin Boko Haram

Mutane 11 sun hallaka, 43 sun jikkata sakamakon harin Boko Haram

Akalla mutane 11 sun rasa rayukansu ranar Lahadi sakamakon harin kunar bakin wake da yan Boko Haram suka kai garin Maiduguri, yayinda akalla mutane 43 suka samu munanan raunuka.

Jaridar Daily Trust ta bada rahoton cewa wasu mata yan kunar bakin wake biyu suka kai wannan mumunan hari a garin Muna, kilomita biyar da birnin Maiduguri.

Wani idon shaida ya bayyana cewa lallai ya ga wadannan yan mata biyu amma bai san yan Boko Haram bane.

Yace: "Ban san yan Boko Haram bane, lallai na gan su suna tafiya a titi. Bal na yi niyyar taimakonsu saboda na yi tunanin cewa baki ne kuma suna neman aiki a wani gida da ke shirin biki."

"Amma ba da dadewa ba, sai na ji tashin Bam, ashe yan matan da na wuce mintuna ashirin da suka wuce ne, yan kunar bakin wake ne. Da rayuwata ta salwanta yanzu."

Hukumomin kawo agaji na gaggawa na jiha da kasa sun kaddamar da taimakon wadanda abin ya shafa inda suka kwashe gawawwaki biyar, sannan wani jami'in JTF ya ce sun kwashe gawawwaki takwas yayinda uku cikin wadanda aka kai asibiti sun kwanta dama.

KU KARANTA: Jiragen yaki sun yi ma yan bindiga luguden wuta a dajin Zamfara

Kakakin hukumar NEMA a Maiduguri, Abdulkadir Ibrahim, a wani jawabi yace: "Jami'an bada agaji na gaggawa sun tabbatar da cewa yan kunar bakin wake biyu ne suka tayar da bam cikin mintuna biyar daga Muna zuwa Daltu da yammacin jiya (6/4/2019)."

"Sakamakon haka, mutane uku sun mutu da yan kunar bakin waken kuma kimanin mutane 41 sun jikkata kuma suna jinya a asibitin Maiduguri."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel