Mun bi tsare-tsaren da ya kamata kafin hukunta yar Najeriya - Saudiyya

Mun bi tsare-tsaren da ya kamata kafin hukunta yar Najeriya - Saudiyya

Ofishin jakadancin Saudiyya a Abuja ta jadadda cewa ta bi dokar ya dace kafin zartar da hukuncin kisa da hukumomin kasar tayi kan yar Najeriya bisa zargin aikata laifuffuka da suka shafi miyagun kwayoyi.

Gwamnatin Tarayyan Najeriya ta hannun babbar mataimakiyar shugaban kasa kan harkokin kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa, a ranar Talata ta caccaki hukuncin kisa da aka zaratar akan matar Najeriya.

Ta bayyana labarin hukuncin kisan a matsayin abun tausayi, abun al’ajabi da bacin rai, inda ya karfafa cewa wassu kamfanonin jirgin sama suna aiki tare da masu safaran kwayoyi wajen saka kwayoyi a jakunkunan fasinjojin.

Mun bi tsare-tsaren da ya kamata kafin hukunta yar Najeriya - Saudiyya

Mun bi tsare-tsaren da ya kamata kafin hukunta yar Najeriya - Saudiyya
Source: Twitter

Amman ofishin jakadancin, a wani jawabi da ta saki a Abuja, ta bayyana cewa an zartar da hukuncin kisan ne bayan an tabbatar da shaida akan zargin.

Sanarwar ta kuma ce an zartar da hukuncin kisar ne bayan an gudanar da bincike mai zurfi kuma an tabbatar cewa laifin da ake tuhumanta da aikatawa ya tabbata.

KU KARANTA KUMA: An matsa wa Goje kan ya amince da Lawan a matsayin Shugaban majalisar dattawa

An tattaro cewa yar Najeriyar ta samu duk wani hakki na doka da ya kamata kafin a yanke mata hukuncin kisa.

Jawabin ya zo kaman haka “Doka ta baiwa dukkan masu laifin dama a kotun shari’a cewa suna da damar daukan lauya da zai iya kare su, kuma masarautan zata dauki nauyin samar da lauyoyi ga duk wanda baya da halin daukar lauya.

"Ana bin dukkan dokoki da tsare-tsaren doka kafin zartar da hukuncin kisa a kasar Saudiyya kamar yadda shari'ar addinin musulunci ya tanada. Wannan shine abinda masarautar Saudiyya ke tafiya a kai," inji sanarwar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel