Sanatocin Niger sun mara wa Lawan baya a tserensa na son zama Shugaban majalisar dattawa

Sanatocin Niger sun mara wa Lawan baya a tserensa na son zama Shugaban majalisar dattawa

Sanatoci masu ci da zababbun sanatoci a jihar Niger karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), a ranar Asabar sun lamuncewa da Sanata Ahmed Lawan a matsayin wanda ya cancanci zama Shugaban majalisar dattawa na tara.

Goyon bayan nasu na kunshe ne a wani jawabi da suka saki a Minna dauke da sa hannun sanatocin uku, Mohammed Sani Musa (Niger ta gabas), Sabi Abdullahi (Niger ta arewa) da kuma zababben sanata, M,uhammad Bima Enagi (Nger ta kudu) a Minna.

A cewarsu, Lawan na da kyawawan hallaya da tarin kwarewa a matsayinsa na dan majalisar da ke kokarin kai majalisar zuwa mataki na ci gaba.

Sanatocin Niger sun mara wa Lawan baya a tserensa na son zama Shugaban majalisar dattawa
Sanatocin Niger sun mara wa Lawan baya a tserensa na son zama Shugaban majalisar dattawa
Source: Twitter

Sun jaddada cewa Lawan na da abubuwan da ake bukata a wajen jagora da shugaba nagari, sannan kuma cewa yana da burin kawo ci gaba a Najeriya da yan Najeriya baki daya.

A wani lamari makamancin haka, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Shugaban APC na kasa, Kwarad Adams Oshiomhole, ya kaddamar a jiya Lahadi, 7 ga watan Afrilu ya bayyana cewa baya ga mukamin Shugaban majalisar dattawa da na kakakin majalisar wakilai da aka riga a kasabta, ba a riga an yi rabe-raben sauran mukaman ba.

Oshiomhole ya kuma bayyana cewa ana duba yiwuwar ba yankin kudu maso kudu mukamin mataimakin Shugaban majalisar dattawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel