'Yan kabilar Ibo sun gaza a siyasar Najeriya - Okorocha

'Yan kabilar Ibo sun gaza a siyasar Najeriya - Okorocha

- Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo ya kalubalanci 'yan kabilar Ibo da rashin nuna godiya dangane da kokarin da jagorori ke yi domin taimakon su

- Okorocha na ci gaba da neman hukumar ta yi abin da ya dacee wajen mallaka masa takardar shaidar cin zabe a matsayin zababben Sanatan shiyyar Imo ta Yamma.

- Gwamna Rochas ya kausasa harshe kan Baturen zabe da ya jagorancin zaben shiyyar Imo ta Yamma da rashin nuna kwarewa aiki

Gwamnan Rochas Okorocha na jihar Imo, ya ce al'ummar kabilar Ibo sun gaza a siyasar Najeriya sakamakon rashin yin amanna da gaskiya da kuma rashin nuna godiya ga jagorori masu fafutikar taimakon su.

'Yan kabilar Ibo sun gaza a siyasar Najeriya - Okorocha

'Yan kabilar Ibo sun gaza a siyasar Najeriya - Okorocha
Source: UGC

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Gwamna Rochas mai barin gado ya bayyana hakan cikin wata sanarwa yayin ganawa da manema labarai a fadar gwamnatin sa da ke birnin Owerri a ranar Litinin, 8 ga watan Afrilu.

Gwamna Okorocha ya ce al'ummar kabilar Ibo sun gaza samun galihu a siyasar Najeriya sakamakon wasu dalilai biyu da suka hadar da rashin riko da gaskiya da kuma rashin yabawa kwazon jagorori masu fafutikar taimakon su.

KARANTA KUMA: Tashin Hankali: Ana girbin sassan jikin Fursunonin Musulmi a kasar China

Okorocha ya kuma nemi hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta watau INEC, da ta gaggauta mallaka ma sa takardar shaidar cin zabe biyo bayan nasarar sa a zaben sanatan shiyyar Imo ta Yamma da aka gudanar a watan Fabrairu.

Cikin kaushin harshe, Gwamna Okorocha ya zargi baturen zabe da ya jagoranci al'amurran gudanar da babban zabe na sanatar shiyyar Imo ta Yamma da rashin nuna kwarewar aiki kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel