Tashin Hankali: Ana girbin sassan jikin Fursunonin Musulmi a kasar China

Tashin Hankali: Ana girbin sassan jikin Fursunonin Musulmi a kasar China

Wani fitaccen marubuci littafai dan kasar Australia da aka haifa a ranar 18 ga watan Yuni, 1973, CJ Werleman, ya shahara wajen sadaukar da rayuwar sa domin bankado ire-iren keta haddi da cin zarafi da ake yiwa Musulmi a Duniya.

CJ Werleman

CJ Werleman
Source: UGC

CJ Werleman ya na ci gaba da bankado irin mummunar ta'adar da ake yiwa musulmi musamman a yankunan da rikici ya zamto masu karfe kafa, ka ma daga rikicin kasar Isra'ila da Falasdinawa, Kashmir, Burma, Syria, India zuwa sansanan gudun hijira na Chechnyna.

Babban marubucin kuma gogaggen dan jaridar ya yi fice wajen bankado yadda ake wulakanta Musulmai a ma'auni na mafi kololuwar cin zarafi musamman fursunoni da ake masu kagen babban laifi inda a cewar sa ya zamto al'ada a yanzu.

Werleman ya yi shaidar cewa, da yawa daga cikin kafofin sadarwa na Yammacin duniya sun kau da idanu a kan wannan mummunan lamari na yiwa Musulmi rashin adalci mai girman gaske a yayin da su ka aikata kananan laifuka da bai taka kara ya karya ba.

Yayin ganawar Werleman da Enver Tohti, wani likitan ilimin halitta dan yankin Uyghur, wani sashe na tarayya kasar China, ya shaida masa yadda ya girbe hanta da kuma koda biyu ta wani fursunan Musulmi a bisa umurni na wani babban likita.

Tohti ya hikaito yadda ya girbe sassan jikin wani fursunan Musulmi bayan da cikin gayya masu zartar hukunci suka harbe sa a barin kirjin sa na dama da manufa ta sheme shi wajen samun damar girbe Hanta da kuma Kodar sa gabanin cikawar sa.

Wannan lamari ya auku ne a shekarar 1995 cikin farfajiyar zartar da hukuncin kisa kan fursunoni ta Urumqi da ke kasar China. Tohti ya ce ya aikata wannan cin zarafi yayin da zuciyar fursanan ke bugawa domin ribatar sassan jikin sa yayin da ya ke raye gabanin ya cika.

Kamar yadda Werleman ya bayyana, Tohti ya shaida masa cewa ya gudanar da wannan aiki a bisa umarni ba tare da yiwa fursanan allurar zamani watau anaestesia mai kashe radadi da zafi na barin jiki da za a yiwa aiki na tiyata.

Tohti ya bayar da shaidar wannan ta'asa a yayin ganawa da manema labarai na wata jaridar kasar Birtaniya a shekarar 2013, inda ya ce wannan lamari ya zamto ruwan dare akan Musulmai musamman na yankin Uyghur.

Shekaru uku bayan aukuwar wannan lamari, Tohti ya tsere daga kasar China bayan ya bayar da shaidar yadda gwaje-gwajen Makaman Nukiliya a yankin Xinjiang ke haifar da hauhawa na adadin masu kamuwa ta cutar Kansa.

A watan da ya gabata cikin wata hira da wata kafar watsa labarai ta Radio Free Asia, Tohti cikin yakini ya bayyana cewa, Attijirai na kasar Saudiya sun kasance mafi akasarin masu ribatuwa da wannan sassan jikin bil Adam da ake girbewa a kasar China.

Sai dai a yayin da dan jarida Werleman ya matsa bincike, Tohti ya yi na'am da rashin kwararan hujjoji da zai yi madogara da su a matsayin shaidar yadda ake cin kasuwar wannan sassan jiki a mayan asibitoci ga Attijirai a kasar Saudiya yayin da rashin lafiya ta sanya su ke neman dashen koda ko kuma hanta ruwa a jallo.

A yayin neman karin bayani dangane da furucin da ya yi yayin ganawa da kafar watsa labarai ta Radio Free Asia, Tohti ya shaidawa Werleman cewa, akwai shaidu da baki ba zai iya furta su ba sakamakon fargabar abin da ka iya kasancewa da Mahaifiyar sa da har ila yau ta na zaune a yankin Xinjiang a can kasar China.

Dakta Faisal Shaheen, shugaban cibiyar dashen sassan jiki na kasar Saudiya, ya shaidawa wata mujalla ta Arabian Business cewa, 'yan kasar Saudiya 410 sun saye sassan jikin bil Adama a tsakanin shekarar 2012 zuwa 2014 ta hanyar gurbatacciyar hanya daga kasashen China, Masar da Kuma Pakistan. Ya ce a halin yanzu akwai marasa lafiya 7,000 da ke bukatar dashen koda a kasar.

Majalisar Turai mai ruwa da tsaki akan kiwon lafiya da kuma kare hakkin dan Adam ta bayyana cewa, ana cin kasuwar kowace koda daya da aka girba ta hanyar da ba ta dace a kan zunzurutun kudi na kimanin dalar Amurka 165,000.

A wannan mako, 'yan majalisar kasar Birtaniya sun yi gargadin cewa, dugunzumammun al'umma masu neman lafiya ta hanyar samun dashen wani sassan jiki su na taimakawa wajen haifar da wannan mummunar al'ada ta cin zarafi da ake yiwa fursunoni musamman a kasashe masu tsarin gwamnati na kwaminisanci.

A yayin da tun karni na 20 kawo yanzu akwai Musulman Uyghur da ke daure a fursunonin yankin Xinjiang da kuma ilahirin kasar China da ya kasance mafi girma ta fuskar yawan adadin fursunonin da ya tara 'yan tsiraran mabiya addini, lamari na cin zarafin Musulmai wajen girbe sassan jikin su ya zamto abin tur da Allah wadai.

KARANTA KUMA: Ricikin kabilanci ya hallaka Mutane 12 a jihar Ebonyi

Da yawa daga cikin mawallafan littafai da su ka shahara a duniya, sun yi ikirarin yadda ake cin zarafi da wulakantar da Fursunonin Musulman Ugyhur a kasar China ta hanyar kisan mummuke da girbe sassan jikin su su na ji kuma su na gani.

Kamar yadda Werleman ya bayyana duk da a cewar sa ba ya da tabbaci, kamfanin jiragen sama na China Southern Airline, ya bayar da rahoton yadda ya yi jigilar fiye da sasan jikin bil Adama 500 tun bayan da Tohti ya bayar da shaidar sa yayin ganawa da jaridar Uyghur Times a watan Maris.

Sai dai ya ce gwamnatin kasar China ta yi karin haske da cewa kamfanin jiragen saman na ta ya na jigilar sassan jikin bil Adama na wadanda su ka bayar a matsayin sadaukarwa domin jin kan al'umma.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel