Ricikin kabilanci ya hallaka Mutane 12 a jihar Ebonyi

Ricikin kabilanci ya hallaka Mutane 12 a jihar Ebonyi

Kimanin rayukan Mutane 12 sun salwanta yayin sabunta wani mummunan rikici na kabilanci a birnin Abakaliki na jihar Ebonyi.

Rincabewar rikici tsakanin kabilar Eyigba ta karamar hukumar Izzi da kuma kabilar Eyibuchiri ta karamar hukumar Ikwo, ta salwantar da rayukan Mutane 12 a birnin Abakaliki na jihar Ebonyi kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ricikin kabilanci ya hallaka Mutane 12 a jihar Ebonyi

Ricikin kabilanci ya hallaka Mutane 12 a jihar Ebonyi
Source: UGC

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, mummunar ta'adar ta auku ne a ranar Asabar, inda wadanda suka riga mu gidan gaskiya su ka yi gamo da ajali a kan hanyar su ta dawowa daga bikin murnar shigar sabbin dalibai jami'ar Ebonyi.

Rahotanni sun bayyana cewa, an yiwa Matafiyan kwanton bauna daura da hanyar jami'ar tarayya ta Alex Ekueme inda aka kone su kurmus cikin motar da ta yo jigilar su. Sai dai ba bu tabbaci na adadin rayukan da suka salwanta.

Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar Ebonyi, DSP Loveth Odah, ya tabbatar da aukuwar ta'addancin tare da cewa tuni kwamishinan 'yan sanda na jihar, Awosola Awotunde, ya kai ziyarar gani da idanu yankin da mummunar ta'adar ta auku.

KARANTA KUMA: An kashe 'yan Najeriya 2 a kasar Afirka ta Kudu

Tuni dai fargaba da zaman ni 'ya su ya mamaye zukatan daliban jami'o'in biyu da kuma Matafiya masu bibiyar hanyar sakamakon fargaba da yiwuwar afkawa cikin gadar zare ta miyagun ababe na sharri.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel