An kashe 'yan Najeriya 2 a kasar Afirka ta Kudu

An kashe 'yan Najeriya 2 a kasar Afirka ta Kudu

A yayin sabunta ta'addanci na nuna kiyayya ga bakin haure a kasar Afirka ta Kudu, mun samu cewa adadin rayukan 'yan Najeriya da ke ci gaba da salwanta na kara hauhawa inda aka kashe wasu Mutane biyu a makon da ya gabata.

Rayukan 'yan Najeriya biyu sun salwanta yayin sabunta ta'addancin nuna kiyayya ga bakin haure a birinin Johannesburg da kuma Cape a tsakanin ranar 5 da kuma 6 ga watan Afrilun 2019 kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

An kashe 'yan Najeriya 2 a kasar Afirka ta Kudu

An kashe 'yan Najeriya 2 a kasar Afirka ta Kudu
Source: Facebook

Kakakin kungiyar al'ummar Najeriya mazauna kasar Afirka ta Kudu, Odefa Ikele, shi ne ya bayar da shaidar aukuwar ta'addancin cikin wata hira ta wayar tarho daga birnin Johannesburg tare da manema labarai a ranar Litinin.

Mista Bonny Iwuoha mai shekaru 48 dan asalin karamar hukumar Ihitte/Uboma ta jihar Imo, ya riga mu gidan gaskiya a yankin kudancin Johannesburg da misalin karfe 11.45 na Yammacin ranar 6 ga watan Afrilu.

KARANTA KUMA: Kotun daukaka kara za ta sake tabbatar da nasara ta a zaben Kano - Ganduje

Kazalika wani dan Najeriya da ajali ya katse masa hanzari a sakamakon ta'addancin kiyayyar bakin haure, Goziem Akpenyi, ya riga mu gidan gaskiya a harabar filin wasanni na BellVille Stadium da misalin karfe 1.00 na ranar Juma'a, 5 ga watan Afrilu a birnin Cape Town.

Aukuwar wannan sabon ta'addanci ya tabbatar da salwantar rayukan al'ummar Najeriya shida kenan yayin da aka harbe wasu Mutane hudu 'yan asalin kasar nan a yankin Sunnyside na garin Pretoria a watan Maris da ya gabata.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel