Kotun daukaka kara za ta sake tabbatar da nasara ta a zaben Kano - Ganduje

Kotun daukaka kara za ta sake tabbatar da nasara ta a zaben Kano - Ganduje

A ranar Lahadin da ta gabata gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, cikin bugun gaba na kyuatata zato ya bayyana cewa, ya na cikakken yakin kotun daukaka kara za ta sake tabbatar da nasarar sa kamar yadda hukumar INEC ta yi.

A yayin da dan takarar gwamnan jihar Kano na jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf, ke ci gaba da kalubalantar karashen zaben da aka gudanar a ranar 23 ga watan Maris, Gwamna Ganduje ya ce kotun daukaka za ta sake tabbatar da nasarar kamar yadda hukumar zabe ta kasa INEC ta yi.

Kotun daukaka kara za ta sake tabbatar da nasara ta a zaben Kano - Ganduje
Kotun daukaka kara za ta sake tabbatar da nasara ta a zaben Kano - Ganduje
Source: Depositphotos

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, Gwamna Ganduje ya bayyana hakan cikin jawaban sa yayin wata hira da manema labarai a birnin Kanon Dabo.

Gwamna Ganduje cikin jawaban sa ya yi zargi da cewar kwamishinan 'yan sanda na jihar Kano, Muhammadu Wakil, ya taka rawar gani wajen bayar da gudunmuwa ta magudin zabe domin rinjayar da nasara zuwa ga jam'iyyar PDP yayin zaben asali na ranar 9 ga watan Maris.

KARANTA KUMA: Cin bashi a kasashen ketare: Kaduna, Legas, Edo da Cross River sun ciri tuta

Gwamnan jihar Kano da ake yiwa lakabi da Khadimul Islama, watau mai yiwa Addinin Musulunci hidima, ya zargi jam'iyyar PDP da ribatar 'yan ta'adda da kuma hukumar 'yan sanda wajen cin karen su ba bu babbaka yayin zaben jihar da aka gudanar a watan da ya gabata.

Kazalika gwamna Ganduje ya yi karin haske kan shirin kafa sabuwar gwamnatin sa a wa'adi na biyu, inda ya ce tuni ya kafa kwamitin da zai jagoranci akala ta shirye-shiryen rantsar da shi karo na biyu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel