Cin bashi a kasashen ketare: Kaduna, Legas, Edo da Cross River sun ciri tuta

Cin bashi a kasashen ketare: Kaduna, Legas, Edo da Cross River sun ciri tuta

Kididdigar cibiyar kula da basussuka ta Najeriya, DMO, Debt Management Office, ta bayyana cewa jihohin Kaduna, Legas, Cross River da kuma Edo, sun sha gaban sauran jihohin Najeriya wajen dora mata kantar bashi da suka ciyo a kasashen ketare.

Binciken da cibiyar DMO ta gudanar ya tabbatar da cewa, jerin jihohin hudu sun ciyo bashi na kimanin $2.12bn cikin $4.23bn da dukkanin jihohin Najeriya 36 da kuma babban birnin tarayya su ka karbo a kasashen ketare.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, jihohin 4 kacal sun karbi bashi na fiye da rabin kaso na bashin da kasashen duniya ke bibiyar gwamnatin Najeriya. Jihohin Legas, Cross River, Edo da kuma Kaduna sun karbi bashi na kaso 50.08 cikin 100 na basussukan da ke kan Najeriya a halin yanzu.

Cin bashi a kasashen ketare: Kaduna, Legas, Edo da Cross River sun ciri tuta

Cin bashi a kasashen ketare: Kaduna, Legas, Edo da Cross River sun ciri tuta
Source: Twitter

A yayin da jihar Legas ke kan gaba da bashin dalar Amurka biliyan 1.43 da ya kasance kaso 33.81%, jihar Edo ta biyo baya da bashi na dalar Amurka miliyan 276.25 da ya yi daidai da kaso 6.53 cikin 100 na nauyin bashi da ke kan gwamnatin Najeriya.

Jihar Kaduna ta biyo bayan jihar Edo inda nauyin bashin da ke kanta ya kai kimanin Dalar Amurka miliyan 227.25 da ya yi daidai da kaso 5.37%. Jihar Cross River ita ce a mataki na hudu cikin jerin jihohin da su ke kan gaba wajen tarawa Najeriya kantar bashi.

Jihar Cross River na da bashin dalar Amurka miliyan 188.77 da ya yi daidai da kaso 4.46 cikin 100 na nauyin bashin da ke kan kasar nan. Sauran jihohin da ke sahun gaba sun hadar da Bauchi($133.93m), Enugu($126.18m), Anambra($107.04m), Ekiti($106.21), Oyo($105m), Ogun($103.26m), Osun($99.08m), Abia($98.58m), da kuma Adamawa($97.79m).

KARANTA KUMA: Ta'addanci: Ana fuskantar baƙin ciki a jihohin Anambra, Zamfara, Katsina, Ribas da Borno

A bashin cikin gida kuma, jihar Legas ta sake cirar tuta inda nauyin bashin da ke kanta ya kai kimanin N530.24bn, yayin da jihar Delta ke take ma ta baya da bashi na N228.81bn. Sai kuma jihar Ribas mai kantar bashi ta N225.59bn.

Sauran jihohin Najeriya masu kantar bashi na cikin gida sun hadar da; Cross River(N167.96bn), Abuja(N164.25bn), Ekiti(N118.01bn), Kano(N117.08bn), Filato(100.37bn) da kuma Imo(98.78bn).

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel