Ta'addanci: Ana fuskantar baƙin ciki a jihohin Anambra, Zamfara, Katsina, Ribas da Borno

Ta'addanci: Ana fuskantar baƙin ciki a jihohin Anambra, Zamfara, Katsina, Ribas da Borno

A yayin sabunta ta'addanci a jihohin Zamfara, Kaduna, Borno, Ribas, Legas, Katsina, da kuma Anambra, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Asabar ya bayyana takaicin sa kan yadda ake ikirarin ba ya damuwa da zubar jinin al'ummar sa.

Gwamnatin tarayya a ranar Asabar ta bayar da umurni a gaggauta dakatar da duk wani hake-hake na albarkatun kasa a jihar Zamfara a yayin da 'yan ta'adda suka hallaka kimanin Mutane hamsin a ranar Talata ta makon da ya gabata.

Ta'addanci: Ana fuskantar baƙin ciki a jihohin Anambra, Zamfara, Katsina, Ribas da Borno
Ta'addanci: Ana fuskantar baƙin ciki a jihohin Anambra, Zamfara, Katsina, Ribas da Borno
Source: Twitter

Salwantar rayuka na ci gaba da auku da a jihar Borno yayin da harin kunar bakin wake na wasu 'yan mata biyu da su ka tayar da bama-bamai ya salwatar da rayukan fiye da mutane goma yayin da kimanin Mutane hamsin su ka jikkata.

A karshen makon da ya gabata cikin birnin Legas, 'yan bindiga sun yi garkuwa da wasu Mutane bakwai da suk hadar da Mata biyu da Maza biyar a yankin Ikosi-Ejirin kamar shugaban hukumar kwana-kwana na jihar, Mista Rasaki Musibau ya bayyana.

Cikin birnin Katsinan Dikko, an gargadi masu yiwa kasa hidima da su tabbatar sun gundara da kai komo da tafiye-tafiyen su cikin ayari sakamakon kalubale na rashin tsaro musamman garkuwa da mutane da ke fuskantar jihar.

Yayin da ta'addanci na garkuwa da mutane da kashe-kashen al'umma musamman yankin Kudancin Kaduna ya yi kamari, mun samu cewa 'yan ta'adda sun hallaka wasu jami'an 'yan sanda biyu bayan sun kai hari ofishin su da kuma kauyen Kakangi dake garin Birnin Gwari.

A can jihar Anambra da ke Kudu maso Gabashin kasar nan, makiyaya sun kai hari kan wata gona a yankin Mmiata Anam da ke karkashin karamar hukumar Anambra ta Kudu inda su ka salwantar da rayukan Mutane biyar yayin da kimanin Mutane 30 su ka jikkata.

KARANTA KUMA: Buhari ya na farin ciki a kan samun nasarar kwato dukiyar kasa - Malami

A yayin mayar da martani da babatu cikin fushi, shugaban kasa Buhari ya jaddada cewa, ba bu wani lamari da gwamnatin sa ta bai wa muhimmanci a halin yanzu face tsananta tsaro domin bayar da kariya ga al'ummar sa da ya zamto nauyi na ka-in-da-la-in da rataya a wuyan sa.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, dara ta ci gida yayin da adawa gami da tsama ta sanya wasu kungiyoyi asiri su ka fafata a tsakanin su cikin birnin Fatakwal inda rayukan Mutane 8 su ka salwanta.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel