Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da yaron wani babban dan siyasa a Abuja

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da yaron wani babban dan siyasa a Abuja

Wasu gungun yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai farmaki har gidan wani babban dan siyasa dake babban birnin tarayya Abuja, Alhaji Yusuf Musa Sokodabo, inda suka yi awon gaba da babban dansa da ba’a bayyana sunansa ba.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da misalin karfe 1 na rana, inda yan bindigan suka kutsa kai gidan dan siyasan dake unguwar Naharati, cikin yankin Abaji.

KU KARANTA: Ranar kin dillanci: Jiragen yaki sun yi ma yan bindiga luguden wuta a dajin Zamfara

Wani shaidan gani da ido daya bayyana sunansa a matsayin Danlami ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya shaida ma manema labaru cewa yan bindigan sun kutsa kai gidan ne ta Katanga, inda suka dauke yaron, sa’annan suka arce dashi ta wani daji.

“Na shiga cikin daji domin na yi fitsari kenan sai na hangi wasu mutane a cikin dajin, na dauka yan kato da gora ne, amma bayan wasu yan mintoci sai kawai na dinga jin karar harbe harben bindiga, da haka na gane masu garkuwa da mutane ne.” Inji shi.

Shima wani daga dangin Sokodabo daya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace tuni suka fara tattaunawa da masu garkuwan, kuma sune nemi a biyasu naira miliyan 5, amma dai suna ta ciniki har zuwa lokacin tattara wannan rahoto.

Amma kaakakin rundunar Yansandan Abuja, ASP Adamu Gajere Tanimu ya bayyana rashin masaniya game da lamarin, sai dai yace zai tuntubi ofishin Yansandan Abaji don jin gaskiyar lamarin.

A wani labarin kuma wasu gungun yan bindiga dauke da muggan makamai sun yi awon gaba da Mista Wellington Magbisa, mahaifin shugaban karamar hukumar Sagbama ta jahar Bayelsa, Honorabul Magbisa Michael.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel