Kudu maso kudu na iya samun mataimakin Shugaban majalisar dattawa - Oshiomhole

Kudu maso kudu na iya samun mataimakin Shugaban majalisar dattawa - Oshiomhole

A yayinda ake ci gaba da gwagwarmaya wajen neman shugabancin majalisun tarayyar kasar a tsakanin shugabannin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), hasashe sun nuna cewa yankin kudu maso kudu na iya samun mukamin mataimakin Shugaban majalisar dattawa na gaba.

Shugaban APC na kasa, Kwarad Adams Oshiomhole, ya kaddamar a jiya Lahadi, 7 ga watan Afrilu cewa baya ga mukamin Shugaban majalisar dattawa da na kakakin majalisar wakilai da aka riga a kasabta, ba a riga an yi rabe-raben sauran mukaman ba.

Oshiomhole ya kuma bayyana cewa ana duba yiwuwar ba yankin kudu maso kudu mukamin mataimakin Shugaban majalisar dattawa.

A hirarsa da jaridar Leadership a daren jiya Lahadi, Oshiomhole da yake magana a hannun kakakinsa, Mista Simon Egbebulem, ya bayyana cewa ba a riga an raba manyan mukaman majalisar ba, amma ya kara da cewa ana duba yiwuwar ba kudu maso kudu mukamin mataimakin Shugaban majalisar dattawa.

Kudu maso kudu na iya samun mataimakin Shugaban majalisar dattawa - Oshiomhole

Kudu maso kudu na iya samun mataimakin Shugaban majalisar dattawa - Oshiomhole
Source: Depositphotos

Akwai rahotannin da ke nuna cewa tuni an rigada an mika mukamin ga yankin kudu maso kudu, musamman ga na hannun daman Oshiomhole, Sanata Francis Alimehkena, wanda aka sake zaba don wakiltan Edo ta Arewa a majalisa na tara.

KU KARANTA KUMA: Ka da APC ta sake ta tsaida ‘Yan takara 2 a Majalisa - Prince Adeyeye

Rahoton ya zarge shi da kokarin bai wa Alimikhen matsayin, amma Shugaban APC ya bayyana hasashen a matsayin ba gaskiya ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel