Ka da APC ta sake ta tsaida ‘Yan takara 2 a Majalisa - Prince Adeyeye

Ka da APC ta sake ta tsaida ‘Yan takara 2 a Majalisa - Prince Adeyeye

Mun samu labari daga Daily Trust cewa Prince Adedayo Adeyeye ya bayyana cewa dole jam’iyyar APC mai mulki ta san yadda tayi, ta tsaida ‘dan takara guda a zaben shugaban majalisar dattawa da za ayi.

Prince Adedayo Adeyeye wanda ya doke Sanata Biodun Olujimi a Ekiti ta kudu a majalisar dattawa ya fito ya bada shawarar yadda jam’iyyar APC za ta karbi shugabancin majalisar tarayya a cikin sauki a zaben bana.

Adedayo Adeyeye mai shirin zama Sanata a APC ya bayyanawa menama labarai cewa jam’iyyar sa ce ya kamata ta karbi shugabancin majalisar dattawa ba tare da tababa ba, a dalilin rinjayen da su ka samu a zaben 2019.

Tsohon Ministan na PDP kuma kakakin jam’iyyar a wani lokaci, ya nuna cewa ya zama dole ‘Ya ‘yan APC su hada-kai a majalisa su marawa wanda ya dace baya domin ganin sun samu nasara a zaben da za ayi kwanan nan.

KU KARANTA: Ya kamata ‘Yan Arewa za su gane shirin Tinubu a Majalisa – Dan Bilki

Ka da APC ta sake ta tsaida ‘Yan takara 2 a Majalisa - Prince Adeyeye

Akwai bukatar Sanatocin APC su hada-kai Inji Adeyeye
Source: Depositphotos

Sabon ‘dan majalisar yayi kira ga APC tayi bakin kokarin ta wajen ganin ta hada-kan Sanatocin ta da ke neman mukamin shugaban majalisar dattawa domin gudun PDP tayi amfani da wannan dama ta nada wanda ta ke so kujerar.

Yanzu haka dai APC ta tsaida Ahmad Lawan inda Sanatocin yankin sa irin su Mohammed Ali Ndume da kuma Mohammed Danjuma Goje su ka nuna sha’awar wannan mukami. Wannan ya sa Adeyeye yake ganin sai an yi sulhu.

A cewar tsohon Ministan, dole sai ana busawa idan an ciza, idan har ana so APC ta kai ga ci. Adeyeye yayi kira ga jam’iyyar sa ta APC da ta zauna da masu neman wannan kujera ta dinke duk wata baraka kafin ranar zabe ya zo.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel