Gungun yan bindiga sun yi awon gaba da mahaifin wani Ciyaman har gida

Gungun yan bindiga sun yi awon gaba da mahaifin wani Ciyaman har gida

Wasu gungun yan bindiga dauke da muggan makamai sun yi awon gaba da Mista Wellington Magbisa, mahaifin shugaban karamar hukumar Sagbama ta jahar Bayelsa, Honorabul Magbisa Michael.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Lahadi, 7 ga watan Afrilu ne yayin da suka dira gidansa da misalin karfe 12 na dare a unguwar Mile 2 cikin garin Sagbama, inda suka yi awon gaba dashi.

KU KARANTA: Marayu 2,073 daga jahar Kebbi sun samu tallafi daga Sarkin Makkah

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa yan bindigan da yawansu ya kai mutum bakwai sun kai farmakin ne dauke da muggan makamai, inda suka kutsa kai cikin gidan mutumin, sa’annan suka fito dashi, suke jefashi cikin kwale kwale, suka bace.

Shima kaakakin rundunar Yansandan jahar Taraba, Butswat Asinim ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace yan bindigan sun samu damar shiga dakin mutumin ne ta wani tagar dakinsa da bashi da kariya.

“Akalla mutane biyar ne suka kutsa kai ta cikin wannan tagar, inda suka dauke shi, sa’annan suka tsere ta cikin ruwa, a yanzu haka an sanar da duk wasu hukumomin tsaro domin bin sawun masu garkuwan tare da kamasu.” Inji shi.

A wani labarin kuma rikicin kabilanci tsakanin kabilun Tibabe da Jukunawa na cigaba da sanadiyyar salwantar rayuka da dama da barnata dukiyoyi a jahar Taraba, inda a wannan karo rikicin ya barke a karamar hukumar Wukari ta jahar.

Rikicin na kwana kwanan nan ya barke ne a kauyukan dake iyaka da jahar Taraba da na Benuwe, inda kabilun biyu suke da rinjaye duka, kamar yadda shugaban karamar hukumar Wukari, Daniel Adi ya bayyana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel