Marayu 2,073 daga jahar Kebbi sun samu tallafi daga Sarkin Makkah

Marayu 2,073 daga jahar Kebbi sun samu tallafi daga Sarkin Makkah

Alheri gadon barci inji masu iya magana, akalla marayu dubu biyu da saba’in da uku ne suka amfana daga wani shirin bada tallafin kudi da gwamnatin kasar Saudiyya a karkashin Sarki Salman ta bayar a jahar Kebbi dake yankin Arewacin Najeriya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito an zabo wadannan marayu ne daga garuruwa guda takwas na jahar Kebbi, daga ciki har da Birnin Kebbi, inda daga nan ne aka fara aikin rabon kudin, kuma babban sakataren kungiyar bada agaji na Musulunci, Dakta Abdul Aziz Bin Ahmad Al-Sarhan da Gwamna Atiku Bagudu suka kaddamar.

Marayu 2,073 daga jahar Kebbi sun samu tallafi daga Sarkin Makkah

Kebbi
Source: Facebook

KU KARANTA: Kotun kolin Najeriya ta shiga halin rudani bisa rahoton ajiye aiki na Alkalin Alkalai

Marayu 2,073 daga jahar Kebbi sun samu tallafi daga Sarkin Makkah

Kebbi
Source: Facebook

Sauran yankunan da suka amfana da shirin sun hada da Gulumbe, Gwandu, Argungu, Jega, Koko, Shanga da kuma Yauri. A jawabinsa, Malam Tahiru Baba Ibrahim da yayi jawabi a madadin babban sakataren kungiyar yace za’a bada kudin ne bisa dadewar rajistan da marayun suka yi a kungiyar.

Yace akwai wasu marayun da suka yi rajista da kungiyar tun shekaru uku da suka gabata, yayin da wasu kuma sai a shekaru biyu da suka gabata suka yi rajista da kungiyar, wasu kuma kasa da haka.

Marayu 2,073 daga jahar Kebbi sun samu tallafi daga Sarkin Makkah

Marayu 2,073 daga jahar Kebbi sun samu tallafi daga Sarkin Makkah
Source: UGC

Shima da yake nasa jawabin, gwamnan jahar Kebbi ya bayyana jin dadinsa da wannan tallafi, inda yace baya ga jahar Borno da Yobe, jahar Kebbi ce ta uku wajen yawan yan gudun hijira, kuma ita ke da yawan almajirai saboda kusancinta da kasashen Nijar da Bini.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel