Shugaban APC ya jahilci yadda mu ke aiki a Majalisa – Sanata Abaribe

Shugaban APC ya jahilci yadda mu ke aiki a Majalisa – Sanata Abaribe

Sanatan Abia ta Kudu a majalisar dattawa, Eyinnaya Abaribe, yayi kaca-kaca da shugaban jam’iyyar APC mai mulki Kwamred Adams Oshiomhole, na kokarin kakabawa majalisar dattawa shugaba a zaben da za ayi.

Sanatan na Abia yake cewa Adams Oshiomhole bai da hurumin da zai zabawa ‘yan majalisar tarayyar kasar wanda zai gaji kujerar Bukola Saraki. Eyinnaya Abaribe yayi wannan bayani ne lokacin da yayi hira da Jaridar Punch.

Sanata Eyinnaya Abaribe yake cewa Adams Oshiomhole ba ya cikin ‘yan majalisa don haka kamata yayi ya ja bakin sa yayi shiru game da wanda Sanatocin kasar za su zaba. Sanatan yace yanzu dole su yi kaffa-kaffa da APC.

A cewar Sanatan, ya kamata a ce shugaban APC ya gane yadda siyasar majalisa ta ke tafiya inda ya so a ce ya kuma ja bakin sa yayi shiru. Abaribe yace Oshiomhole bai taimaki Sanatocin sa na APC da matakin da ya dauka ba.

KU KARANTA: Ya kamata ‘Yan Arewa za su gane shirin da Tinubu yake yi a Majalisa - Bilki

Shugaban APC ya jahilci yadda mu ke aiki a Majalisa – Sanata Abaribe

Abaribe yace Oshiomhole bai san harkar zaben Majalisa ba
Source: Twitter

Jam’iyyar APC ta bakin shugaban na ta, ta fito tace dole ‘Ya ‘yan ta su marawa Sanata Ahmad Lawan da kuma Honarabul Femi Gbajabiamilla a majalisar dattawa da ta wakilai. Wasu ‘Yan APC kan su ba su yi na’am da wannan ba.

Shi dai Eyinnaya Abaribe ya nuna cewa ‘Yan majalisar PDP za su bude idanun su da kyau game da duk wani wanda APC ta zakulo ta ke nema ya rike ragamar majalisar. Abaribe yace doka ba ta ba APC damar yi wa Majalisa kutse ba.

Sanatan ya goyi bayan maganar Ali Ndume da yace doka ba ta ba APC damar ta-cewa a majalisa ba. A karshe Sanatan yace har yanzu PDP ba ta gama yanke shawarar wanda za ta marawa baya a zaben shugabannin majalisar ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel