Bai kamata a kyale Tinubu yayi duk abin da yake so a APC ba – Dan Bilki

Bai kamata a kyale Tinubu yayi duk abin da yake so a APC ba – Dan Bilki

Babban ‘dan siyasar nan Abdulmajid Danbilki wanda yana cikin Jagororin jam’iyyar APC a Arewacin Najeriya ya fito yayi magana game da tirka-tirkar siyasar majalisar tarayya ta 9 da za a kafa.

Alhaji Danbilki Commander ya bayyana cewa bai dace a kyale Asiwaju Bola Tinubu yayi karfa-karfa wajen kakaba yaran sa a matsayin shugabannin majalisar dattawa da kuma na wakilan tarayya a wannan karo ba.

Bilki Commander yake cewa Bola Tinibu yana yunkurin rika jan akalar siyasar Arewa da jam’iyyar APC ta hanyar nada na-kusa da shi a kan shugabacin majalisar tarayya. Commander yace lokaci yayi da ya kamata a farga.

KU KARANTA: 2019: Siyasar Majalisa tana daukar wani sabon salo a Najeriya

Bai kamata a kyale Tinubu yayi duk abin da yake so a APC ba – Dan Bilki

Dan Bilki yace ba za su bari Tinubu ya rike linzamin APC ba
Source: Depositphotos

A wani jawabi da Commander ya fitar a Kano, kamar yadda mu ka samu labari, yayi kira ga ‘yan siyasar da ke Arewa cewa su zare kan su daga sarkakiyar hannun Bola Tinubu, wanda ya ke neman ganin kowa yayi yadda yake so.

Dan Bilki Commander ya nuna cewa mutanen Arewa ba za su cigaba da biyewa ra’ayin Bola Tinubu a tafiyar APC ba, domin kuwa a ta bakin sa, kowa yana da ‘yancin nemawa kan sa zabin da ya dace da shi a siyasar Najeriya.

Babban ‘Dan a-mutun na shugaba Buhari ya kuma kara da cewa, babu dalilin da za a bari ra’ayin wani mutum tal, ya zarcewa abin da sauran ‘yan jam’iyya su ke hari. Yanzu APC dai tana shirin ganin ta kafa na-ta a majalisa ta 9.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel