Shugaban kasa da Saraki sun tafi kasashen Larabawa, Osinbajo yana Rwanda

Shugaban kasa da Saraki sun tafi kasashen Larabawa, Osinbajo yana Rwanda

A karshen makon nan ne mu ka ji cewa manyan shugabannin Najeriya, sun tattara sun fice daga kasar inda aka bar shugaban majalisar wakilan tarayya watau Rt. Hon. Yakubu Dogara kadai a cikin gida.

A Ranar Lahadin nan da ta wuce watau 7 ga Watan Afrilun 2019, an yini ne babu shugaban kasa, da mataimakin sa da kuma shugaban majalisar dattawa a Najeriya. Wanda kurum ya rage shi ne Kakakin majalisar wakilan kasar.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bar Najeriya tun Juma'a inda ya halarci wani taron tattalin arziki na Duniya a kasar Jordan, a Ranar Lahadi ne kuma shugaban kasar ya biya Birnin Dubai a cikin kasar UAE domin wani taron na-dabam.

KU KARANTA: Shugaban kasa Buhari ya bar Birnin Amman ya isa Dubai

Shugaban kasa da Saraki sun tafi kasashen Larabawa, Osinbajo yana Rwanda

Shugaban kasa Buhari da sauran masu iko ba su gida
Source: Facebook

Shi kuma mataimakin shugaban kasar watau Farfesa Yemi Osinbajo, ya bar Najeriya ne zuwa kasar Ruwanda inda yake halartar wani bikin cika shekaru 25 da shudewar yaki da rikicin basasa da aka yi a kasar Ruwandar ta Afrika.

A na sa bangaren, shu kuma Bukola Saraki, wanda shi ne na 3 a jeringiyar masu mulki a Najeriya, yana kasar Qatar wajen wani taro na kungiyar ‘yan majalisa na Duniya. Saraki ya halarci taron ne a matsayin sa na shugaban majalisar kasar.

Sai dai duk da cewa manyan shugabannin na Najeriya sun bar gida, ba a mikawa Yakubu Dogara mulki ba. Majiyar tace babu bukatar wani ya karbi ragamar ikon kasar tun da shugaba Buhari ba hutun aiki ko yawon ganin Likita ya tafi ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel