'Yan daba sun datse hannayen wani dalibin jami'ar Usman Danfodiyo, hotuna

'Yan daba sun datse hannayen wani dalibin jami'ar Usman Danfodiyo, hotuna

Wasu matasa da ake zargin 'yan daba ne sun datse hannayen wani dalibi, Habibu Abubakar, da ke shekara ta biyu a sashen karatun yaruka turai a jami'ar Usman Danfodio da ke jihar Sokoto.

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewar 'yan dabar sun yiwa dalibin kwanton bauna da sanyin safiyar ranar Lahadi tare da kwace masa babur dinsa kafin daga bisani su datse masa hannayensa guda biyu.

Abubakar Attahiru, mahaifin dalibin, ne ya tabbatar da faruwar hakan majiyar mu, ya bayyana har yanzu ba a san su waye suka aikata hakan ga dan nasa ba.

'Yan daba sun datse hannayen wani dalibin jami'ar Usman Danfodiyo, hotuna

Hannayen dalibin jami'ar Usman Danfodiyo
Source: Twitter

'Yan daba sun datse hannayen wani dalibin jami'ar Usman Danfodiyo, hotuna

Dalibi Habibu Abubakar
Source: Twitter

'Yan daba sun datse hannayen wani dalibin jami'ar Usman Danfodiyo, hotuna

'Yan daba sun datse hannayen wani dalibin jami'ar Usman Danfodiyo
Source: Facebook

Da yake magana cikin halin dimuwa, Attahiru ya ce; "wasu yan daba sun tare shi da misalin karfe 2:00 na safiyar ranar Lahadi, sun kwace masa babur dinsa, sannan sun datse masa hannaye, sun bar shi kwance cikin jini.

DUBA WANNAN: Yadda farfelar jirgin sojin sama ta hallaka babban soja mai suna Umar

"Dan uwana aka fara sanarwa bayan abin ya faru, kuma an gaggauta kai shi asibitin kashin na Wammako domin ceto rayuwar sa."

Ba a samu jin ta bakin Mohammed Abubakar, kakakin rundunar 'yan sanda na jihar Sokoto, ba har ya zuwa lokacin da aka wallafa wannan labari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel