'Yan bindiga sun sace shugaban hukumar kashe gobara ta jihar Legas

'Yan bindiga sun sace shugaban hukumar kashe gobara ta jihar Legas

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da darektan hukumar kashe gobara ta jihar Legas, Rasaki Musibau, tare da wasu mutane 9 a kan titin Epe zuwa Itokin dake Ikorodu da yammacin ranar Asabar.

Lamarin, kamar yadda rahotannu suka bayyana, ya faru ne a yayin da shugaban da ragowar mutanen ke kan hanyar su ta dawowa cikin garin Legas daga Epe.

Jaridar The Nation tarawaito cewar masu harkuwa da mutanen sun tare kan gadar Itokin, tare da kaddamar da harin kwanton bauna a kan mutanen da ke cikin motoci guda uku.

A wata ruwayar, mazauna yankin sun yi zargin cewar an sace wasu mutanen a cikin wata babbar mota da ke safarar mutane a tsakanin kashe bayan motar ta tsaya domin sauke wasu fasinjoji a kan hanyar.

Wani mazaunin yankin da ya yi maga da jaridar The Nation, ya ce motar ta tsaya ne domin sauke wasu fasinjoji a Ejirin, bayan saukar su wasu daga cikin mutanen dake tsaye gefen hnaya suka shiga cikin motar domin karasa wa Legas.

'Yan bindiga sun sace shugaban hukumar kashe gobara ta jihar Legas

'Yan bindiga sun sace shugaban hukumar kashe gobara ta jihar Legas
Source: Twitter

"Lamarin ya faru ne ranar Asabar da misalin karfe 7:00 na yamma. Daya daga cikin motocin da ke safara tsakanin kasashe ta tsaya domin sauke wasu fasinjoji, bayan ta sauke su ne sai wasu fasinjojin suka shiga.

"Ashe mutanen da suka shiga motar masu garkuwa da mutane ne, kuma su ne suka tafi da motar da mutanen cikinta zuwa wurin da babu wanda ya sani ya zuwa yanzu.

DUBA WANNAN: Satar mutane a hanyar Abuja zuwa Kaduna: Matafiya sun koma tafiya a jirgin sama

"Wannan lamarin daban yake da batun satar shugaban hukumar kashe gobara. Su an sace su ne ta hanyar yiwa ayarinsu kwanton bauna yayin da suke dawowa Legas daga Epe. Wannan yanki nema yake ya koma mai hatsari.

"Mun shiga damuwa matuka saboda dawowar aiyukan garkuwa da mutane da tsagerun yara ke yi," a cewar mutumin.

Kazalika, ya yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su kawo masu agaji kafin lamarin ya girmama.

DSP Bala Elkana, kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Legas, ya tabbatar da sace Musibau da ragowar mutanen dake cikin tawagar sa. Ya bayyana cewar an sace mutanen bayan an yiwa motoci uku da suke ciki kwanton bauna.

Sannan ya kara da cewa jami'an 'yan sandan da aka tura wurin sun yi nasarar samun wasu kayayyaki na mutanen da aka sace.

Elkana ya kara da cewa kwamishinan 'yan sandan jihar Legas, Bala Zubairu, ya ziyaci wurin da kansa kuma. Ya ce an tura rundunar 'yan sanda ta musamman domin kubutar da mutanen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel