Satar mutane a hanyar Abuja zuwa Kaduna: Matafiya sun koma tafiya a jirgin sama

Satar mutane a hanyar Abuja zuwa Kaduna: Matafiya sun koma tafiya a jirgin sama

Matafiya sun cigaba da cika tasahar jiragen kasa a Abuja da Kaduna, duk da hobbasa da shugaban rundunar 'yan sanda (IGP), Mohammed Adamu, ya yi wajen kafa wata rundunar atisaye ta musamman da aka yiwa da 'Operation Puff Adder', a ranar Juma'a, domin magance satar mutane da hana aiyukan ta'addanci a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Matafiya sun cika a tsahar jirgin kasa ta Idu a Abuja da ta Rigasa a Kaduna da duku-dukun ranar Asabar domin samun damar yankan tikitin jirgi.

Dogon layin jama'a ya bawa matafiyan mamaki, saboda sun yi tunanin ganin cewar Asabar ce, za a samu saukin cunkuson jama'a.

Satar mutane a hanyar Abuja zuwa Kaduna: Matafiya sun koma tafiya a jirgin sama
Matafiya sun koma tafiya a jirgin kasa
Source: Twitter

Satar mutane a hanyar Abuja zuwa Kaduna: Matafiya sun koma tafiya a jirgin sama
Matafiya a layin sayen tikitin jirgi
Source: Twitter

Satar mutane a hanyar Abuja zuwa Kaduna: Matafiya sun koma tafiya a jirgin sama
Matafiya a tashar jirgin kasa
Source: Twitter

Satar mutane a hanyar Abuja zuwa Kaduna: Matafiya sun koma tafiya a jirgin sama
Matafiya a tashar jirgin kasa ta Kaduna
Source: Twitter

Wani matafiyi da ya ce sunansa Abdullahi ya shaidawa majiyar mu cewar: "na yanke shawar yin tafiya yau (Asabar) saboda sanin cewar an fi samun cunuson jama'a ranar Juma'a, amma sai gashi yau an samu cunkuso duk da ranar hutun karshen mako ce. Hakan ya nuna cewar mutane basu da tabbacin tsaron lafiyar su idcan suka yi amfani da hanyar mota.

An fuskanci karancin tikiti saboda samun karuwar matafiya a jirgin kasa.

DUBA WANNAN: Yadda farfelar jirgin sojin sama ta hallaka babban soja mai suna Umar

Wani mutum da ya zo tashar jirgin kasa dake Abuja tare da iyalinsa ya bayyana cewar; "tun misalin karfe 5:00 na safe na tashi domin na zo da wuri na samu tikiti, ina tunanin zan isa Kaduna kafin karfe 9:00 na safe."

Mutumin ya bayyana cewar babu tabbacin ko zai yi bukaguro zuwa Kaduna saboda ya rasa tikitin jirgin.

Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kara adadin taragon jiragen domin su samu damar daukan mutane da yawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel