Dr. Bashir Omar ya fadawa Shugaba Buhari ya ka kafa dokar ta baci a Jihar Zamfara

Dr. Bashir Omar ya fadawa Shugaba Buhari ya ka kafa dokar ta baci a Jihar Zamfara

- An nemi Gwamnatin Tarayya ta kafa dokar ta-baci a cikin Jihar Zamfara

- Matsalar rashin tsaro a Jihar ya sa wani babban Malami yayi wannan kira

- Limamin Masallacin Al-Furqan, Dr. Bashir Omar ya bada wannan shawara

Labari ya zo mana cewa babban Limamin Masallacin nan na Al-Furqan da ke cikin Garin watau Dr. Bashir Omar yayi kira ga gwamnatin tarayyar Najeriya ca ta tashi tsaye a game da rikicin da ake ta fama da shi a Jihar Zamfara.

Limamin na masallacin Al-Furqan ya fadawa shugaban kasa Muhammadu Buhari a hudubar sa ta Juma’a cewa yayi kokari wajen ganin an kawo karshen satar jama’a ana garkuwa da su, da kuma kashe-kashe da ake yi a Zamfara.

Dr. Bashir Omar yayi wannan kira ne a hudubar da yayi a kan mimbarin Juma’ar nan a Ranar 5 ga Watan Afrilun 2019. Sheikh Bashir Omar ya nemi gwamnatin kasar ya kafa dokar ta-baci a jihar Zamfara domin ganin an samu zaman lafiya.

KU KARANTA: An hallaka Bayin Allah wajen biki a Garin Birnin Gwari

Malamin yana gani hakan ne kawai zai kawo karshen wannan kashe-kashe da ake tayi babu kaukautawa a jihar ta Zamfara. Shehin Malamin yace ya dade yana yin wannan kira domin ganin an hukunta masu wannan danyen aiki.

Malamin yake cewa ya kamata a ga aiki da cikawa a gwamnatin shugaba Buhari wajen kawo karshen garkuwa da mutane ana karbar kudin fansa daga hannun su. Sheikh Omar ya koka da cewa satar jama’a ya zama hanyar samun kudi a yau.

Hudubar Malamin ta jawo hankalin shugaba Buhari da cewa babu yadda kasa za ta iya cigaba a cikin rashin tsaro. Hakan dai yayi dai-dai da irin kiran da wani fitaccen Malamin, Dr. Ahmad Gumi yayi kwanaki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel